Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ayyana ranar Laraba 19 ga watan Yuli 2023 a matsayin ranar ɗaya ga watan Muharram na sabuwar shekarar 1445H.
Sultan, Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, tun farko ya buƙaci Musulmi da su sanya ido kan ganin jinjirin watan Muharram a ranar Litinin, 17 ga Yuli, 2023.
Al-Muharram shi ne watan farko a kalandar Musulunci kuma ana ganin wata ne mai alfarma.
An umurci musulmi da su gudanar da azumin a ranakun 9 da 10 ga wata, wanda ake ƙira Tasu’a da Ashura.
KU KUMA KARANTA: Malaman addini a Malawi sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da auren jinsi
Ita ma wannan ranar tana da mahimmaci domin ta kasance ranar da Allah ya ceci Annabi Musa daga hannun Fir’auna na Masar, inda ya ƙetare Teku tare da mutanensa.
Majalisar Sarkin Musulmi ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 18 ga Yuli, 2023.
“Saboda rashin samun ingantaccen rahoton ganin jinjirin watan a Najeriya, an ayyana ranar Laraba 19 ga watan Yuli 2023 a matsayin ranar farko ta MUHARRAM 1445H,” in ji sanarwar.