Hukumar EFCC ta kama ‘yan ƙasar China 13 bisa laifin haƙo ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a Kwara

0
367

Rundunar shiyar Ilorin na hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa, (EFCC), ta ce ta kama wasu ‘yan ƙasar China 13 da ake zargi da aikata ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a jihar.

Wilson Uwujaren, kakakin hukumar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Ilorin ranar Alhamis.

Waɗanda ake zargin sun haɗa da mace ɗaya da maza 12 kuma an kama su ne a ranar Larabar da ta gabata a Unguwar Gwamnati da ke Ilorin.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta kama ma’aikatan FMC 50 bisa zargin zamba ta intanet a jihohin Ogun da Oyo

Mista Uwujaren ya lissafa waɗanda ake zargin sun haɗa da: Guo Ya Wang mai shekaru 36 da Lizli Hui mai shekaru 42 da Guo Jian Rong mai shekaru 36 da Lizh Shen Xianian mai shekaru 37 da Lishow Wu mai shekaru 26 da Guo Pan mai shekaru 38 da kuma Lia Meiyu mai shekaru 53. Sauran sun haɗa da: Guo Kai Quan, mai shekaru 36, Lin Pan, mai shekaru 50, Ma Jan, 38, Wendy Wei Suqin, 31, Li Zhinguo Wei, 29 da Xie 53.

“Wannan ya biyo bayan sahihan bayanan sirri game da ayyukansu, waɗanda suka haɗa da amma ba’a iyakance ga haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, rashin biyan kuɗaɗen sarauta ga Gwamnatin Tarayya kamar yadda doka ta tanada,” in ji Uwujaren.

Ya ce an kama su ne sakamakon bincike na gaskiya da aka yi a kan ayyukan masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a Kwara.

Kakakin ya bayyana cewa, ma’aikatan suna da wuraren haƙar ma’adanai daban-daban ba bisa ƙa’ida ba a kusan dukkanin ƙananan hukumomi 16 na jihar.

“Bayan an yi musu tambayoyi, waɗanda ake zargin sun amsa cewa ma’aikatan wani kamfani ne na ƙasar China mai suna W. Mining Global Service Limited, da ke Olayinka a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar.

“An tattaro cewa kamfanin yana amfani da ɗanyen da ake haƙowa ba bisa ƙa’ida ba wajen samar da marmara da kuma sayar da shi a cikin gida Najeriya.

“Bincike ya kuma nuna cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargi da ke aiki a kamfanin ba su da izinin aiki, amma sun zo da takardar izinin ziyarta daga China zuwa Abuja kuma sun yi tafiya ta hanyar Ilorin,” inji shi.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne muƙaddashin shugaban hukumar EFCC Abdulkarim Chukkol ya koka da yadda masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a wasu sassan ƙasar nan.

Ya bayyana hakan a matsayin babban barazana ga tattalin arziƙin gida da na ƙasa. A watannin baya-bayan nan, hukumar EFCC na shiyyar Ilorin ta kama mutane 80 da suka yi ba bisa ƙa’ida ba tare da kama manyan motoci 24 na ma’adanai daban-daban.

A ranar 10 ga Satumba, 2022 ne rundunar ‘yan sandan ta kama wani ɗan ƙasar China, Dang Deng, Manajan Darakta na Sinuo Xinyang Nigeria Ltd., da laifin mallakar wasu tan 25 na ɗanyen ma’adanai daban-daban.

Daga bisani mai shari’a Mohammed Sani na babbar kotun tarayya da ke Ilorin ya yanke masa hukunci a ranar 19 ga watan Oktoba.

Leave a Reply