Su waye suka sace fitilun titin tashan jirgin sama na Legas?

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ɓarayi sun sace fitilun titin ɗaya daga cikin filayen jiragen saman Najeriya watanni bayan an saka su.

Mahukunta a filin tashin jiragen saman ne suka tabbatar wa da BBC aukuwar wannan lamari.

Tuni aka ƙaddamar da bincike don kama waɗanda suka aikata wannan sata da kuma dawo da abin da suka sata.

Ba dai a san lokacin da aka sace fitilun a filin tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas ba.

Kodayake wasu kafafan yaɗa labaran jihar sun ce ana zargin ma’aikatan filin jirgin saman da hannu a wannan sata.

KU KUMA KARANTA: Wasu ‘yan bindiga sun kashe ma’aikacin INEC, sun sace matarsa a Ebonyi

A watan Nuwambar 2022 ne, aka sanya fitilun domin ƙara haske a filin.

Saboda duhun wajen dole aka mayar da jiragen da ke zirga-zirga a tsakanin jihohin Najeriya sauƙa da tashi a ɓangaren tashin jiragen ƙasashen waje.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *