An sace mahaifar ta, bayan ta haihu a wani asibiti a Ondo

Rundunar ‘yan sanda a jihar Ondo ta kama wata ma’aikaciyar jinya, ma’aikaciyar lafiya da kuma mai gadi a cibiyar lafiya ta ‘Comprehensive Health Centre’, da ke garin Emure-IIe, a ƙaramar hukumar Owo, bisa ga wani abin al’ajabi na ɓacewar mahaifar wani jariri.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Olufunmilayo Odunlami-Omisanya, ya bayyana cewa an kama mutanen uku ne bayan mahaifin jariri mai shekaru 23, Tunde Ijanusi, ya koka kan lamarin a ofishin ‘yan sanda na Emure-Ile. 

Ya ce mahaifiyar mai shayarwa ‘yar shekara 19 ta haifi ɗiya mace a ranar 15 ga watan Yuni a cibiyar lafiya kuma lokacin da mahaifin jaririn ya nemi a ba shi mahaifa, ma’aikaciyar jinya da mataimakinta sun kasa yin bayani inda mahaifar take. 

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe basaraken gargajiya da ‘ya’yansa huɗu, sun sace shanu 100 a Kaduna

Da yake zantawa da manema labarai, mahaifin jaririn, Ijanusi, ya ce ya damu matuƙa bayan da ma’aikatan lafiya da suka ɗauki nauyin haihuwa suka ka sa ba su mahaifar jariri kamar yadda aka saba.  

Ita ma da take magana, kakar mahaifin jaririn, Misis Funmilayo Ijanusi, ta ce bayanai da jami’an asibitin suka bayar na cewa wai wani Kare ya shiga cikin ɗakin ya yi awon gaba da mahaifar ba abin yarda ba ne.  

Ta ce jami’an ma’aikatan cibiyar sun yi ƙoƙarin shawo kan ‘yan uwa da su yi haƙuri su bar maganar, su kuma asibiti za ta sallami mahaifiyar jaririyar ba tare da an karɓi ko sisi ba.


Comments

2 responses to “An sace mahaifar ta, bayan ta haihu a wani asibiti a Ondo”

  1. […] KU KUMA KARANTA: An sace mahaifar ta, bayan ta haihu a wani asibiti a Ondo […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: An sace mahaifar ta, bayan ta haihu a wani asibiti a Ondo […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *