Matata ta auri wani mutum a asirce – miji ya shaida wa kotu

1
467
Ta kama mijinta yana lalata da ’ya’yan cikinsu

Wani ɗan kasuwa Chuka Emmanuel a ranar Alhamis ya maka matarsa ​​Jane a gaban wata kotun gargajiya da ke Jikwoyi Abuja bisa zargin auren sirri.

Mista Chuka wanda ya shigar da ƙara a cikin takardar sakinsa, ya ce: “matata ta bar gidanmu ba tare da ta sanar da ni ba.

Daga baya na sami sabon wurin da take, da na isa wurin na gane cewa ta auri wani mutum kuma ta riga ta haifi ɗa da shi.

“A kan haka ne nake neman raba auren da ke tsakaninmu,” in ji shi.

Ya shaida wa kotun cewa matarsa ​​ta bar shi da ‘ya’yansu uku tun shekarar 2020.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta ɗaure wata mata mai shekaru 57, kan laifin yi wa yaro ɗan shekara 8 fyaɗe

“Ni ne mai kula da yaran, bana son wani ya sanya min guba a raina, ina roƙon wannan kotu da ta hana matata zuwa gidana don ganin ‘ya’yana ba na nan.

“Ina roƙon wannan kotu mai daraja da ta raba auren kuma ta ba ni riƙon ‘ya’yana maza uku.” Ya roƙe shi.

Alƙalin kotun, Labaran Gusau, ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har sai ranar 22 ga watan Yuni domin ci gaba da sauraron ƙarar.

1 COMMENT

Leave a Reply