Nan da 12 ga watan Yuni za mu kammala aikin kwasan maniyyata aikin Hajji – Aero Contractors

0
569

Kamfanin jiragen sama na ‘Aero Contractors’, a ranar Lahadi ya ce zai kammala jigilar maniyyatan Najeriya dubu 8,033 da aka ware masa don aikin Hajjin shekarar 2023 nan da ranar 12 ga watan Yuni.

Liman Mohammad, jami’in kula da aikin hajji na 2023 ga ‘yan kwangilar Aero, ya bayar da tabbacin a cikin wata sanarwa da ya fitar. Mohammed ya ce hukumar alhazai ta ƙasa NAHCON ta ware maniyyata 8,033 ga kamfanin domin jigilar su zuwa ƙasar Saudiyya.

KU KUMA KARANTA: Hajj 2022: Jihar Kaduna Za Ta Yi Jigilar Maniyata Aikin Hajjin Bana 2491

A cewarsa, mahajjatan sun fito ne daga jihohin Nasarawa da Oyo da Adamawa da kuma Taraba. Ya ce tuni kamfanin ya kammala jigilar dukkan alhazan jihar Nasarawa zuwa Saudiyya.

Jami’in ya ƙara da cewa ya zuwa yanzu, kamfanin ya yi jigilar maniyyata 2,748 daga jihohin Nasarawa da Oyo. Ya ce kamfanin ya koma Legas inda zai yi jigilar maniyyata kusan 1,500 daga jihohin Oyo da Legas a cikin jirage biyar.

Mohammed ya ce, kamfanin jirgin ya ƙuduri aniyar kammala jigilar dukkan alhazan da aka tura shi zuwa ranar 12 ga watan Yuni, mako biyu kafin rufe filin jirgin na Jeddah.

“Don haka daga ranar 12 ga watan Yuni za mu gama.

Za a rufe filin jirgin sama na Jiddah a ranar 26 ga watan Yuni, wato kimanin kwanaki 14 da kammala aikinmu, da yardar Allah,” inji shi.

Leave a Reply