Jami’an hukumar ƴan sandan ciki na Najeriya DSS sun yi wa ofishin hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasar zagon-ƙasa a Lagos dirar-mikiya inda suka hana jami’an na EFCC shiga ofishin a Ikoyi.
Duk ƙoƙarin jin ta bakin masu magana da yawun hukumomin biyu ya ci tura.
Kafofin yaƴa labarai na ƙasar sun ruwaito cewa daman akwai saɓani a tsakanin hukumomin biyu a kan wadda a tsakaninsu ta mallaki ginin.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wani jami’in DSS ya faɗa mata bisa sharaɗin ɓoye sunansa cewa daman sun daɗe suna taƙaddama da EFCC a kan wadda ta mallaki ginin, wanda su DSS ne suke amfani da shi tun ma kafin a ƙirƙiri EFCC kuma ya ce an mallaka wa DSS ɗin.
KU KUMA KARANTA: Ayi hattara da ‘hukumar EFCC na bogi’ – EFCC
Jami’in ya ƙara da cewa batu ne da yake a tsakanin hukumomin biyu, kuma bai je gaban shari’a ba sannan ba su taɓa rikici a kai ba kafin yanzu.
”To amma yanzu ba mu san dalilin da suka zo suka hana jami’anmu shiga ofishin ba, duk da cewa ga sabuwar gwamnati ta zo,” in ji shi.
Jaridar ta ce duk ƙoƙarin ji daga bakin masu magana da yawun hukumomin biyu Wilson Uwujaren na EFCC, da kuma Dakta Peter Afunaya na DSS a kan batun bai yi nasara ba.