Buhari ya naɗa Sha’aban Sharaɗa a matsayin shugaban hukumar lura da ilimin almajirai da ƙananan yara

Daga Ammar Muhammad Rajab

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a jiya Lahadi ya naɗa ɗan majalisar Tarayya mai barin gado mai wakiltar ƙaramar hukumar Kano Municipal, Hon. Sha’aban Sharada a matsayin shugaban sabuwar Hukumar lura da Almajirai da waɗanda ba sa zuwa makaranta.

Da yake sanar da naɗin ga manema labarai, mai magana da yawun shugaban ƙasa, Mallam Garba Shehu, ya ce naɗin ya biyo bayan amincewar da shugaban ƙasa ya yi ne a kan ƙudirin dokar 2023 na bayar da ilimi ga almajirai da ƙananan yara da ba sa zuwa.

Sharaɗa dai ya yi Digirinsa na farko a ɓangaren aikin jarida a Jami’ar Bayero ta Kano, sannan kuma ya yi Digiri na biyu a fannin harkokin kasuwanci daga Jami’ar Chichester a Birtaniya.

Awanni kafin kammala wa’adin mulkinsa, Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar kula da almajiranci.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Buhari ya yi jawabin ban kwana ga ‘yan Najeriya

Majalisar wakilai ta Nijeriya ce ta fara amincewa da dokar kafin ta kai gaban shubaban, inda ya rattaɓa mata hannu.

Dokar dai na neman samar da tsarin ilimi mai kyau da bunkasa fasahar koyon sana’o’i da kuma rage talauci tsakanin almajirai a Nijeriya.

Har ila yau, dokar za ta kuma kyautata karatun tsangaya da rayuwar almajirai da sauran yaran da ke gara-ramba ba su zuwa makaranta.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *