An hana Ganduje da Soludo shiga wurin manyan baki na alfarma a Eagle Square

0
199

Gwamnan jihar Kano mai barin gado, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gamu da cikas a bukin rantsar da sabon shugaban ƙasa a Eagle Square da ke Abuja.

Ganduje da matarsa Hafsat sun yi ƙoƙarin shiga cikin wurin da ake keɓe wa manyan baƙi masu alfarma amma sai jami’an tsaro suka dakatar da shi suka ce takardar gayyatar da yake da ita koriya ce kuma sai mai takardar gayyata mai ruwan gwal ne zai shiga cikin wannan ɓangaren.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Buhari ya yi jawabin ban kwana ga ‘yan Najeriya

Ya jira na tsawon fiye da minti 10 kafin ya ɗauki ƙaddara ya koma ɓangaren da aka tanadar wa baƙi irinsa.

Shi ma gwamnan jihar Anambara, Charles Soludo ya yi ƙoƙarin shiga wannan ɓangaren amma kamar Ganduje shi ma jami’an tsaro sun taka masa birki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here