Ayi hattara da ‘hukumar EFCC na bogi’ – EFCC

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta gargaɗi ‘yan Najeriya game da sanarwar ‘damfara’ da wasu marasa gaskiya suka yi ta hannun hukumar EFCC na ƙarya.

Faɗakarwar zamba na iya kasancewa ta hanyar ƙiraye-ƙirayen ƙarya da aka ce ta fito ne daga teburin taimakon hukumar.

Kakakin ta, Wilson Uwujaren, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata, inda ya ce ‘saƙon damfara’ da ake ta yaɗawa a shafukan sada zumunta na bogi ne.

KU KUMA KARANTA: Buhari ya ƙaddamar da hedikwatar hukumar kwastam, ya lanƙwame sama da biliyan 19

“Don kaucewa shakku, EFCC ba ta da irin wannan tebur, kuma duk wani bayani da ake zaton ya fito daga hukumar EFCC HELP DESK ba ta samo asali daga EFCC ba.

“Yin amfani da EFCC da mawallafin saƙon damfara ya yi na mugun nufi. “Yana da muhimmanci a sanar da jama’a, domin hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba idan har wani ya zama wanda aka zalunta a fili ta hanyar zamba.

“Don haka hukumar ta shawarci jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da tantance duk wani bayani da ke da alaƙa da su,” inji shi.


Comments

4 responses to “Ayi hattara da ‘hukumar EFCC na bogi’ – EFCC”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Ayi hattara da ‘hukumar EFCC na bogi’ – EFCC […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Ayi hattara da ‘hukumar EFCC na bogi’ – EFCC […]

  3. […] KU KUMA KARANTA: Ayi hattara da ‘hukumar EFCC na bogi’ – EFCC […]

  4. […] KU KUMA KARANTA: Ayi hattara da ‘hukumar EFCC na bogi’ – EFCC […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *