A watan Yuli za mu fara samar da man fetur – Ɗangote

0
329

Shugaban rukunin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya bayyana cewa sabuwar matatar man Ɗangote da aka ƙaddamar za ta samar da kason farko na albarkatun man fetur ga kasuwa kafin ƙarshen watan Yuli.

Attajirin ɗan kasuwar nan na Najeriya ya bayyana haka ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata a wajen bikin ƙaddamar da aikin matatar man, mai 650,000 a kowace rana (BPD), aikin haɗaka da matatar mai da ke yankin Lekki na yankin ciniki maras shinge na jihar Legas.

Haɗin matatar man fetur da rukunin sinadarai za su samar da ayyukan yi kai tsaye dubu 9,500 da kuma wasu 25,000. Da yake jawabi a wurin bikin, Ɗangote ya ce bikin ƙaddamar da wani sabon salo ne mai ƙayatarwa ga ɓangaren mai da iskar gas na Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Hamshaƙin ɗan kasuwa Ɗangote, ya gina babbar matatar mai a Najeriya

Ya ce: “Akwai ƙwarin guiwarmu cewa za mu kwaikwayi a wannan fanni abin da a zahiri muka samu a kasuwannin siminti da takin zamani yayin da Najeriya ta sauya daga kasancewar ta kan gaba wajen shigo da waɗannan ɗanyen kayayyaki zuwa masu fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.

“Manufarmu ta farko ita ce, mu zage damtse hasashen samar da kayayyaki iri-iri domin tabbatar da cewa a cikin wannan shekarar, mun samu damar biyan buƙatun al’ummarmu na samar da ingantattun kayayyaki, don ba mu damar kawar da bala’in dogaro da shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje, mu daina gaba ɗaya. Ya zama a kasuwanninmu na kayayyakin mai da ba su da inganci.

“Kayan mu na farko za su kasance a kasuwa kafin karshen watan Yuli, farkon watan Agustan wannan shekara. “Kamfanin zai tabbatar da cewa ana sarrafa da gudanar da mafi girma da ƙarfi na mai, me amfani da inganci don baiwa matatar damar yin gasa da kasuwannin mai.”

Leave a Reply