No menu items!

Sample Page Title

Date:

‘Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma tara a Unguwar Danko kusa da ƙauyen Dogon Dawa a yankin Birnin Gwari a Jihar Kaduna, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A cewar jaridar, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a lokacin da waɗanda abin ya shafa ke aiki a gonakinsu.

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wasu manoma kusan uku zuwa wani wuri da ba a san ko a ina ba ne.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kai hari a jami’ar Filato – Jami’a

Zaɓaɓɓen memba mai wakiltar mazaɓar Kakangi, Yahaya Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce duk waɗanda aka kashe manoma ne, kuma waɗanda suka samu raunukan harbin bindiga an garzaya da su asibiti domin yi musu magani.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...