El-Rufa’i ya rushe asibiti, makarantu da gidajen jama’a ƙasa da sati ɗaya ya bar mulki

Da misalin karfe 1:30 na daren ranar Lahadi 21 ga watan Mayun 2023, tawagar hukumar tsara birane ta jihar Kaduna, wato KASUPDA ta rushe asibitin Kauthar da aka gina domin al’umma da makarantun Fudiyya dake Rimi, Danmadami, Tudun Wada, da gidan Alhaji Musa Birnin Yero da kuma gidan Alhaji Sulaiman Bala. Sun yi wannan ɗanyen aiki ne bisa umarnin gwamna mai barin gado Nasiru El-Rufai.

Wasu ganau sun shaidawa wakilinmu cewa jami’an rushe muhallan sun tattake Alƙur’ani mai girma tare da rushe gine-ginen kan Alƙur’anan.

KASUPDA ba su bayar da wata sanarwa ko raba wata takarda na dalilin rushe muhallan ba kamar yadda Muhammad Rabiu ya shaidawa wakilinmu a Kaduna.

KU KUMA KARANTA: Zan ci gaba da korar ma’aikata, da rushe gine-gine har zuwa rana ta ƙarshe a ofis – El-Rura’i

Idan ba ku manta ba, kafafen watsa labaran Nijeriya sun labarto cewa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya amince da rushe muhallan waɗanda ya kira da ‘IMN’ amma shi yana muhallan nufin mabiya Shaikh Zakzaky da kuma wasu gine-gine dake Gbagyi da waɗansu wurare duk a jihar ta Kaduna ƙasa da mako biyu ya kammala mulkinsa a jihar ta Kaduna.

El-Rufai ya amince da rushe waɗannan muhallai ne a wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 20 ga Afrilun 2023. Inda hukumar KASUPDA ke neman Naira 29,253,500 da kuma jami’an tsaro sama da dubu biyu domin gudanar da wannan aikin rushe-rushen.

Cikin adadin wannan kuɗin, hukumar ta KASUPDA na da buƙatar Naira miliyan 20,253,500 domin rushe muhallan da ya kira na ‘IMN’.

Sai dai a wata takardar ƙarar da aka shigar a gaban babbar kotun Kaduna mai ɗauke da lamba KDH/KAD/515/23; makarantun Imam Sadiq Academy LTD, Tahfiz Fudiyyah Zaria, Fudiyyah Nursery and Primary Schools., Saminu Kusa Muhammed, Ahmad Abubakar, Haruna Danfulani U/Mu’azu, Shuhada Foundation, a madadinsu da kuma ‘Yan Shi’a mazauna jihar Kaduna sun maka gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Gwamnatin jihar Kaduna, Ma’aikatar Gidaje da ci gaban Birane ta jihar Kaduna, KASUPDA, da kuma Daraktan KASUPDA, Isma’il Umaru Dikko a gaban kotun ne bisa yunƙurin da suke yi na rusa musu muhallai ba bisa ƙa’ida ba da kuma sunan cewa na ‘IMN’ ne.

Masu shigar da ƙarar sun ce waɗannan muhallai ba su da alaƙa ta kusa ko ta nesa da abin da waɗanda aka maka gaban kotun suke iƙirari. Inda suka nemi kotun da ta dakatar da su.

Ƙarar wanda aka shigar a gaban babbar kotun jihar Kaduna, har wala yau ƙara neman da kotun ta bayar da umurnin hana rushe musu muhallai da sunan cewa na ‘IMN’ ne. Inda suka ce gine-ginensu ne da suka gina bisa ƙa’idar doka, kuma suna da dukkanin wani shaida na yin gini a jihar ta Kaduna.

Sannan sun kuma nemi kotun da ta ci tarar waɗanda ake ƙara inda aka same su da wannan laifi bisa wannan yunƙuri da suka yi na rusa musu muhallai.

Wakilinmu ya shaidi shaidar shigar da ƙarar wacce aka gabatar a gaban babbar kotun na Kaduna ɗauke da kwanan wata 18 ga watan Mayun 2023.

El-Rufai ya yi alwashin zai ci gaba da rushe-rushe da korar ma’aikata har zuwa ranarsa ta ƙarshe a ofis.


Comments

2 responses to “El-Rufa’i ya rushe asibiti, makarantu da gidajen jama’a ƙasa da sati ɗaya ya bar mulki”

  1. […] KU KUMA KARANTA: El-Rufa’i ya rushe asibiti, makarantu da gidajen jama’a ƙasa da sati ɗaya ya bar mulki […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: El-Rufa’i ya rushe asibiti, makarantu da gidajen jama’a ƙasa da sati ɗaya ya bar mulki […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *