An haifi jariri na farko ta hanyar IVF a Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya

3
285

Sashin Magungunan Haihuwa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zariya, an shirya shi don samar da In-Vitro Fertilisation, (IVF), wato a ɗebo maniyyin namiji a zuba a ƙwan mace kuma ta samu ciki ta haihu.

Farfesa Adebiyi Adesiyun na sashen kula da magungunan haihuwa na ƙungiyar ‘IVF Project’, ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ranar Alhamis a Zariya.

Mista Adesiyun ya bayyana hakan ne a kan ci gaban da ABUTH ta samu, a matsayin asibitin gwamnati na farko a yankin Arewa maso Yamma da ya samu haihuwa wanda aka yi amfani ta hanyar IVF.

Ya ƙara da cewa an haifi jariri namiji da ƙarfe 10:53 na safiyar ranar 16 ga watan Mayu mai nauyin kilogiram uku (3kg). Duk da an fuskanci ƙalubale iri-iri amma an yi nasara.

KU KUMA KARANTA: Yadda mace mai ciki ta mutu a asibitin Kano sakamakon rashin takardun kuɗi

“Duk da haka, idan aka yi la’akari da waɗannan ƙalubalen ƙungiyar ta tuntuɓi babban Daraktan Likitoci, Farfesa Hamid Umdagas, da shawarar yin haɗin gwiwa da wani asibiti mai zaman kansa, don ba da wannan magani ga jama’a,” in ji shi.

Ya ce hukumar ce ta wajabta kuma an yi wannan aikin na farko ne tare da haɗin gwiwar wata cibiyar kula da haihuwa a Kaduna.

A cewarsa, haɗin gwiwar ya ta’allaƙa ne kan amfani da ɗakin gwaje-gwajen haihuwa na cibiyar haihuwa mai zaman kanta da ke Kaduna, wajen tattara ƙwan mata da maniyyin maza domin samun ciki a haihu.

Ya bayyana cewa an yi sauran abubuwan da suka shafi jinya da kula da marasa lafiya a ABUTH. “Mun fara ba da daɗewa ba, mun yi keke biyu kuma muna da wasu marasa lafiya da ke jiran karɓar magani.

“Muna da asibitoci a ranar Litinin, idan kun zo za ku iya ganin adadin marasa lafiya da ke son a musu hakan,” “in ji shi.

Ya ce manufar sashen ita ce a samu cikakkiyar cibiyar haihuwa inda kuɗin hidimar zai yi sauƙi sosai.

Shi ma da yake jawabi, wani memba na ƙungiyar, Farfesa Solomon Avidime, ya ce sashin kula da lafiyar haihuwa na asibitin yana da isasshen ƙarfin da zai iya biyan buƙatun mutanen da suke son ɗaukar ciki.

Mista Avidime ya ce babban abin da ke damun su shi ne samar da kuɗaɗe, musamman don ginawa da samar da kayan aikin da ake shirin samarwa a cibiyar haihuwa a ABUTH.

Ya bayyana cewa akwai ƙalubale wajen samun tallafin daga ƙasashen waje domin ƙasashen da suka ci gaba na ganin cewa yawan jama’a shi ne matsalar Najeriya ba ƙarancin al’umma ba, wanda hakan zai sa a yi wahala a samu tallafin da ƙasashen waje ke yi wa waɗannan ayyuka.

“Muna buƙatar gwamnati ta fahimci cewa akwai gungun mata da maza, waɗanda ke shan wahala saboda ba su da ‘ya’yan nasu.

“Wannan rukunin mutane ne kawai za su iya samun yara ta hanyar fasahar IVF, don haka ya kamata gwamnati ta kawo musu agaji ta samar musu da ayyukan yi.

Ya ce mahukuntan ABUTH sun taimaka; tana ƙoƙarin kafa cikakkiyar cibiya ta haihuwa ƙarƙashin haɗin gwiwar jama’a masu zaman kansu, don samar da ayyukan da ake samu da sauƙi.

3 COMMENTS

Leave a Reply