Kotu ta umarci GTBank ta biya naira miliyan 5 ga Muhuyi Rimingado daga asusun gwamnatin Kano

0
238

Kotun ƙolin masana’antu ta ƙasa da ke Abuja ta umarci GTBank da ta biya korarren shugaban hukumar ƙorafe-ƙorafen jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, kuɗi Naira Miliyan 5,713,891.22 daga asusun albashi na gwamnatin jihar.

Adadin kuɗaɗen da Rimingadon yake bi ne na albashin ma’aikata, bayan dakatar da shi a watan Yulin 2021.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ta dakatar da Muhuyi Rimingado bayan buɗe bincike kan wasu kwangiloli da ake zargin an baiwa wasu kamfanoni masu alaƙa da iyalan gwamnan.

KU KUMA KARANTA: An maka magini a kotu, bisa laifin satar buhunan siminti 50

A zaman da aka ci gaba da yi a ranar Talatar da ta gabata, bankin ta bakin lauyansa Joshua Shekwolo ya shaida wa kotun a cikin wata takardar rantsuwa cewa gwamnatin jihar Kano ta na da asusun ajiyar banki da jimillar kuɗaɗen da suka kai N5,713,891.22 kasancewar an toshe hukuncin da aka yanke kan lamarin a cikin asusun.

Da yake bayar da cikakkiyar umarnin, mai shari’a O.O Oyewumi ya umarci GTBank ta biya kuɗin a asusun Rimingado cikin sa’o’i 48.

An bayar da umarnin ne bayan gazawar gwamnatin jihar wajen mutunta hukuncin da kotun ta yanke a ranar 14 ga Disamba, 2022, inda ta bayar da umarnin biyan da kuma amincewa da Rimingado a matsayin ƙwararren shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

Leave a Reply