Najeriya na shirin kwashe ɗalibanta daga ƙasar Sudan

1
1136

Abike Dabiri-Erewa, shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, (NIDCOM), ta ce hukumar na shirin kwashe ‘yan Najeriya daga Sudan. Sai dai ta bayyana cewa ba zai yiwu kowane jirgi ya tashi ba a wannan lokaci.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Gabriel Odu, mai magana da yawun hukumar NIDCOM, ya fitar a Abuja.

Mis Dabiri-Erewa ta ce, Ofishin Jakadancin Najeriya a Sudan da ‘Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa’, (NEMA), sun tsara shirin kwashe ɗalibai da ‘yan ƙasar da suka maƙale a Sudan.

KU KUMA KARANTA: Ɗaliban Najeriya a Sudan sun nemi a kwaso su daga ƙasar

Ta ce halin da ake ciki a Sudan ya sanya ya zama “haɗari kuma ba zai yiwu ba ga kowane jirgin sama a wannan lokacin”. A cewarta, jiragen da aka ajiye a filin jirgin sun ƙone.

Ta kuma ce ƙungiyoyin agaji na neman hanyoyin samun abinci, ruwa da magunguna ga mutane. Ta yi ƙira ga ɓangarorin da ke rikici da juna da su yi la’akari da yarjejeniyar zaman lafiya ta Juba da ƙungiyar raya ƙasashe ta IGAD ta bayyana.

Ta ce yarjejeniyar wani muhimmin tsari ne na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar. Dakarun Sudan da dakarun ‘Rapid Support Forces’ (RSF) a ranar Alhamis daban-daban sun ba da sanarwar tsagaita buɗe wuta na sa’o’i 24 amma an ci gaba da gwabzawa bayan wa’adin.

Koyaya, an ba da rahoton cewa ƙarfin ya ragu sosai a safiyar Asabar. Rikicin Sudan dai wani rikici ne da ke ci gaba da gudana tsakanin ɓangarorin gwamnatin sojan Sudan da ke adawa da juna.

An fara shi ne a ranar 15 ga Afrilun 2023, lokacin da rikici ya ɓarke a faɗin ƙasar, musamman a babban birnin ƙasar Khartoum da kuma yankin Darfur.

Faɗa ya ƙara tsananta a kusa da filin jirgin saman babban birnin ƙasar, tare da rufe sararin samaniyarsa, da kuma kusa da asibitoci, lamarin da ya kawo cikas ga yunƙurin kwashe mutanen da kuma jinyar waɗanda suka jikkata.

Dubban mutane ne suka jikkata. Har ila yau, fararen hula na kokawa da katsewar wutar lantarki da kuma ƙarancin abinci.

An kuma dakatar da ayyukan agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya.

1 COMMENT

Leave a Reply