An maka magini a kotu, bisa laifin satar buhunan siminti 50

6
971
Ta kama mijinta yana lalata da ’ya’yan cikinsu

Wani magidanci mai shekaru 34, Segun Bashiri, a ranar Alhamis, ya gurfana a gaban wata kotun majistiri ta Okitipupa dake jihar Ondo bisa zargin satar buhu 50 na simintin Ɗangote wanda kuɗinsa ya kai N235,000.

Wanda ake ƙarar, wanda ba a bayar da adireshinsa ba, yana fuskantar tuhuma biyu, wanda ya shafi aikata laifuka da sata.

Ɗan sanda mai shigar da ƙara, ASP Zedekiah Orogbemi, ya shaida wa kotun cewa wanda ake ƙara da ɗaya wanda har yanzu ba a garƙame shi ba a ranar 12 ga watan Janairu da misalin ƙarfe 12:30 na safe a wani gini da ke kan titin Okitipuoa-Ikoya a cikin Okitipupa, sun haɗa baki wajen aikata laifi da kuma sata.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun ceto mutane 5, sun kama 17 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Nasarawa

Mista Orogbemi ya ce wanda ake ƙara da sauran manyan ma’aikata ne a wani gini, mallakin wani Mathew Kawonise, sun sace buhunan siminti da aka yi niyyar yin aiki dasu.

A cewar sa, laifukan ana hukunta su ne a ƙarƙashin sashe na 412 da 390(9) na kundin laifuka, Cap. 37, Vol. 1, Dokokin Jihar Ondo, 2006. Sai dai wanda ake tuhumar ya ƙi amsa laifin da ake tuhumarsa da shi. Alƙalin kotun, Mista Chris Ojuola, ya bayar da belin wanda ake ƙara a kan kuɗi N100,000, tare da mutane biyu da za su tsaya masa.

Ojuola ya ce dole ne waɗanda za su tsaya masa su kasance a ƙarƙashin ikon kotun kuma su gabatar da shaidun biyan haraji na shekaru biyu da aka yi wa gwamnatin jihar.

Daga nan ya ɗage ci gaba da sauraren ƙarar har zuwa ranar 6 ga watan Mayu.

6 COMMENTS

Leave a Reply