Buhari ya isa birnin Madina don gudanar da umara da ziyarar aiki

1
242

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Madina na ƙasar Saudiyya domin fara ziyarar aiki ta kwanaki takwas a ƙasar ta Gabas ta Tsakiya.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, jirgin shugaban ƙasar da ke jigilar shugaban Najeriya da wasu muƙarrabansa ya tashi daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja da ƙarfe 9:10 na safiyar ranar Litinin, ya sauka a filin jirgin saman Yarima Mohammed Bin Abdullaziz na Madina da misalin ƙarfe 17:00 na dare agogon gida.

KU KUMA KARANTA: NAHCON ta sanar da kuɗin aikin Hajjin bana

A lokacin da yake Madina, shugaban zai gudanar da salloli biyar na rana da kuma sallar tarawihi a masallacin Nabawi kafin ya tashi zuwa Makkah da Jeddah, da yammacin ranar Laraba, domin gudanar da aikin Umara.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban ƙasar a ranar Litinin a wata sanarwa ya bayyana cewa ziyarar aiki ta bana daga 11 zuwa 19 ga watan Afrilu ita ce ziyarar Buhari ta ƙarshe a masarautar a matsayin shugaban ƙasa.

NAN ta ruwaito cewa shugaban ya kammala aikin Umrah ne a shekarar 2021.

1 COMMENT

Leave a Reply