Sarkin Musulmi ya yi kira ga Malamai da Fastoci su guji wa’azin raba kan ‘yan Najeriya

0
250

Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce wasu ‘yan barandan siyasa na barazana ga tarihin Najeriya da na al’ummarta.

A cikin wani saƙon taya murna na bikin Easter da Sarkin Musulmin ya aika wa shugaban Ƙungiyar Kiristocin Najeriya, Daniel Okoh, ya ce lamarin ‘aiki ne na Shaiɗan, wanda makircinsa mai rauni ne.’ Kamar yadda Alƙur’ani ya bayyana.

A cikin jawabin nasa, wanda ya samu sa hannun Mataimakin shugaban Majalisar Ƙoli ta Lura da Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Farfesa Salisu Shehu, Sarkin ya buƙaci shugaban na CAN ya haɗa hannu da Ƙungiyar ta Musulunci wajen ganin an rage yadda limamai da fasto-fasto ke cusa wa mabiyansu ƙiyayya ta siyasa da kuma ta addini.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya ta gargaɗi Peter Obi akan yunƙurin kawo cikas ga zaman lafiyar ƙasa

Daga ƙarshe mai alfarma Sarkin Musulmin ya taya al’ummar Kirista murnar zagayowar ranar Easter tare da addu’ar Allah ya ci gabantar da Najeriya.

Leave a Reply