‘Yan bindiga sun sace matasa 80 a Zamfara 

0
197

Matasan da ba su gaza 80 ba, waɗanda suka shiga cikin daji ɗebo itatuwan girki sun shiga hannun ‘yan ta’adda da ake zaton sun yi garkuwa da su a jihar Zamfara. 

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa lamarin, wanda ya auku a ƙauyen Wanzamai da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Jumu’an nan ya jefa mutanen ƙauyen cikin firgici da tashin hankali.

Duk wani yunƙurin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar ko gwamnatin Zamfara ya ci tura har zuwa yanzu da muke haɗa wannan rahoton.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 3 a Legas – ‘Yan sanda

Amma iyayen da aka yi garkuwa da ‘ya’yansu sun shaida wa BBC Hausa a wata hira cewa yan ta’addan sun sace matasan yaransu maza da mata yayin da suka je ɗebo Itace a daji.

A cewar wani mahaifi, “Lamarin ya shafi kowa a ƙauyen, ko dai ɗanka ko ɗiyarka na cikin waɗanda ke tsare a hannun ‘yan ta’adda, ko kuma ‘ya’yan yan uwanka. Ni kaina sun tafi da ɗana da Babur ɗina.” 

Wata mata a ƙauyen Wanzamai ta ce ɗiyarta ‘yar shekara 15 a duniya na cikin waɗanda aka yi garkuwa da su. 

“Mun shiga damuwa saboda ba mu san halin da ‘ya’yanmu suke ciki ba a hannun ‘yan bindiga,” inji ta. 

Har kawo yanzun da muka kawo muku wannan labarin ‘yan ta’addan ba su tuntuɓi kowa game da neman kuɗin fansa ba.

Bayanai sun nuna cewa ‘yan ta’adda sun kai hari a baya farkon watan Ramadan kan mazauna ƙauyen Wanzamai amma dabbobi kaɗai suka sata suka yi gaba.

Leave a Reply