No menu items!

Sample Page Title

Date:

A ranar talata 28/03/2023 da ne aka gano gawar wata mace kwance a bakin titi a ƙauyen Anadariya da ke ƙaramar hukumar Bebeji a kan hanyar Kano zuwa Jos a jihar Kano.

Bayan samun rahoton ne kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Mamman Dauda ya umurci tawagar jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin SP Tanimu Wada, jami’in ‘yan sanda (DPO) na Bebeji da su bibiyi lamarin.

KU KUMA KARANTA: Za a rataye wani ɗan aiki da ya kashe tsohuwa, da ‘yarta

Nan take rundunar ta garzaya wurin da lamarin ya faru inda suka kai gawar zuwa babban asibitin Tiga inda wani likitan lafiya ya tabbatar da rasuwar ta.

A cewar mai magana da yawu rundunar yan jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa, binciken farko da aka gudanar an gano sunan marigayiyar mai suna Theresa Yakubu mai shekaru 20 da haihuwa mai ɗauke da cikin wata biyu, kuma ta zaune ne a ƙauyen Anadariya da ke ƙaramar hukumar Bebeji.

“Har ila yau binciken ya kai ga gano saurayinta,Philibus Ibrahim, mai shekaru 20 ɗan Unguwar Korau a ƙaramar hukumar Tudun Wada da abokinsa, Gabriel Bila, ɗan shekara 25, wanda su ke zaune a gida ɗaya.

“A binciken da ake yi, Philibus ya furta cewa ya yi wa budurwar ciki ne watanni biyu da suka wuce, kuma duk ƙoƙarin da suka yi na zubar da cikin ya ci tura, sai ya haɗa baki da abokinsa ya kai ta wani daji, abokin ya ta riƙe hannunta, shi kuma ya yi amfani da ɗan kwalinta ya shake ta har lahira.” Ina ji Abdullahi Kiyawa.

Zuwa yanzu dai an mayar da shari’arsu zuwa sashen binciken manyyan laifukan na jihar (SCID), domin zurfafa bincike kafin daga bisa ni a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...