Ana tuhumar wata mace kan laifin zagin shugaba Macron a Facebook

Wata mata a arewacin Faransa za ta gurfanar a gaban ƙuliya bisa zargin cin mutuncin shugaba Emmanuel Macron na ƙasar Faransa bayan ta bayyana shi a matsayin ‘jaza’ a wani sakon da ta wallafa a Facebook, kamar yadda mai gabatar da ƙara ya bayyana a ranar Laraba.

Matar na fuskantar tarar Euro 12,000 kwatankwacin Naira miliyan 6 da dubu ɗari 24 amma ba ɗauri ba idan aka same ta da laifi a shari’ar da za a yi a watan Yuni.

An kama ta ne a ranar Juma’a kuma aka tsare ta a gidan yari domin amsa tambayoyi bayan da ofishin kula da ƙananan hukumomi na jihar ya shigar da ƙara kan shafinta na Facebook, kamar yadda mai gabatar da ƙara a garin Saint Omer da ke arewacin ƙasar, Mehdi Benbouzid ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

KU KUMA KARANTA: Za a rataye wani ɗan aiki da ya kashe tsohuwa, da ‘yarta

Koken dai ya mayar da hankali ne kan wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar 21 ga Maris, kwana daya kafin Macron ya yi wata hira da gidan talabijin na TF1 a lokacin cin abincin rana domin kare sauye-sauyen kuɗaɗen fansho da ya janyo cece-kuce a fadin ƙasar.

Matar ta rubuta cewa “Wannan ƙazantar za ta yi magana da ku da karfe 1:00 na rana … kullum a talabijin ne muke ganin wannan ƙazanta”.

Matar mai shekaru 50, ta kasance mai goyon bayan zanga-zangar “Yellow Vest” na shekarar 2018 zuwa 2019 da ta girgiza Macron a lokacin wa’adinsa na farko.

Ana tuhumarta da “cin mutuncin shugaban ƙasar Faransa” kuma za a gurfanar da ita a ranar 20 ga watan Yuni a Saint Omer, in ji mai gabatar da ƙara.

“Suna so su ba da misali da ni,” matar ta shaida wa jaridar yankin La Voix du Nord wadda ta fara ba da rahoton zargin.

Matar wadda jaridar ta bayyana sunanta Valerie, ta ce ta yi matukar mamaki da ta amsa ƙwanƙwasa ƙofar da aka yi mata a safiyar Juma’a, inda ta tarar da ‘yan sanda sun zo su kama ta.

“Na tambaye su ko wasa ne, ba a taɓa kama ni ba.

“Ni ba makiyin jama’a ba ce lamba daya.” In ji ta.

Zanga-zangar da aka kwashe watanni ana yi na nuna adawa da sake fasalin fensho ya haifar da dagula al’amura a Faransa kuma Macron da gwamnatinsa sun ƙi ba da kai bore ya hau.

Wani sabon rikici ya ɓarke tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zanga a ranar Talata, kuma ƙungiyoyin ƙwadago sun sanar da sabuwar ranar yajin aiki da zanga-zanga a ranar 6 ga Afrilu.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *