‘Nakan shafa hoda don ɓoye tabon dukan da mata ta kemim tsawon shekaru 20’ – Ba Ingile

Wani ɗan ƙasar Birtaniya mai shekaru 46, Richard Spencer, ya bayyana yadda yake yin shafe shafen kayan kwalliya don ɓoye raunukan da matarsa ​​Sheree take ji masa yayin da take masa dukan tsiya.

Richard ya bayyana wasu faifan bidiyo na cin zarafi da dukan da matarsa ke masa waɗanda aka ɗauka ta kyamarar tsaro a ɗakin wasan yara.

A lokacin wata hira, Richard ya ce, “Idan na tuna waɗannan abubuwan, ba na jin inada alaƙa da su, kamar sun faru da wani ne bani ba. Na san ni ne, amma a raina, na kasa fahimtar yadda na bari wannan abun ya faru dani.

KU KUMA KARANTA: Mijina yayi wa ubana dukan kawo wuƙa, ya ɓata mini sana’a

“Nakan sanya kayan shafe shafe don in ɓoye raunuka, zagi ya zama ruwan dare.”

Sheree, mahaifiyar ƙananan ‘yan mata uku kuma babbar manaja a ma’aikatar shari’a, tana fuskantar hukunci kan “mafi munin shari’a na cin zarafi da kuma tilastawa,” in ji Alƙalin da ke kula da shari’ar.

An yanke mata hukuncin zaman gidan yari na shekaru huɗu a kotun Hull Crown bayan ta amsa laifin tilastawa da sarrafa hali da kuma tuhume-tuhume uku na cin zarafi da suka shafi cutar da jiki.


Comments

One response to “‘Nakan shafa hoda don ɓoye tabon dukan da mata ta kemim tsawon shekaru 20’ – Ba Ingile”

  1. […] KU KUMA KARANTA: ‘Nakan shafa hoda don ɓoye tabon dukan da mata ta kemim tsawon shekaru 20’ – Ba Ingile […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *