Magoya bayan jam’iyar LP na yunƙurin mamaye ofisoshin hukumar zaɓe

1
331

Jam’iyyar labour (LP) ta zargi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) bisa bita da ƙulle da ta ce hukumar na yi mata, ta kuma nuna rashin jin daɗi game da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

A wani taron manema labarai da jam’iyyar ta shirya a Legas, kakakin kwamitin yakin neman zaben ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Dr. Yunusa Tanko, ya zargi INEC da kin bin umarnin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa da ta umurce ta da ta baiwa jam’iyyar da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi damar duba sakamakon zaɓen da hukumar ta tattaro.

KU KUMA KARANTA: 2023: Obi da Datti sun sha alwashin zuwa kotu

Tare da duba da kuma mallakar kwafi na gaskiya na kayan da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaɓen.

Ya ce kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta bai wa hukumar ta INEC umarnin ne ranar 3 ga Maris duk da cewa hukumar ta kasance da wakilci a kotun lokacin da aka ba da umarnin, amma sai tayi kunnen uwar shegu ta umarnin.

Yunusa Tanko ya ce jam’iyyar ta kuma aike da wasika zuwa ga Hukumar a ranar 6 ga Maris, inda ta tunatar da alƙalan hukumar zaɓen cewa har yanzu ba ta bi wannan umarni ba.

Kakakin jam’iyyar ta Labour ya yi barazanar cewa jam’iyyarsu za ta nemi magoya bayanta da su gudanar da zanga-zangar lumana a ɗaukacin al ofisoshin hukumar da ke fadin ƙasar nan saboda kin bin umarnin kotu da hukumar tayi.

“Ya kamata a lura da cewa a dimokuradiyya irin tamu, dole ne bin doka ya yi nasara ba kawai a tsarin shari’armu ba, har ma a tsarin tsarin jikinmu baki daya.

“Masu shari’a irin na nan take dole su yarda su bi duk wani umarnin kotu da gaskiya kuma kada a ga wani ɓangare ya yi amfani da taimakon kai don tozarta ko rashin mutunta umarnin kotu wanda idan ba a bincika ba tare da takaita shi ba zai iya kawo cikas ga dimokuradiyyar mu da bin doka da tsarin mulki.

“Hakanan matakin da INEC ta ɗauka ya kasance ga dukkan dalilai, mataki ne na rashin bin doka da kuma kin bin umarnin kotu da gangan,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, yayin da INEC ta hana jam’iyyar Labour duba takardun zaɓen, hukumar ta fara gyara na’urorin BVAS ba tare da wakilan jam’iyyu sun halarci harabar ba domin tabbatar da bayanan tare da ganin su da ido kafin hukumar ta share su daga na’urar VBAS.

“Saboda haka muna kira ga jama’a da su lura da matakin rashin bin doka da oda, da rashin bin umarnin kotu da wata muhimmiyar hukuma irin ta INEC ta yi, wanda kuma wani yunƙuri ne da aka kitsa na ɓatawa da kuma daƙile gabarar karar da jam’iyyar labour da ɗan takararta na shugaban ƙasa Peter Obi ya kai a gaban kotu.

“Saboda haka muna son mu bayyana cewa ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen kiran magoya bayanmu da su yi takakkiya cikin lumana zuwa ofisoshin INEC a faɗin ƙasar nan don gudanar da zanga-zangar lumana, domin nuna wa duniya aibun matakin INEC na ƙin bin doka da oda, wannan shi ne matakin da zamu ɗauka domin dakile bijirewa umarnin kotu da INEC ta yi,” in ji shi.

Dr. Tanko wanda ya ci gaba da cewa, Obi ya lashe zaɓen shugaban ƙasa domin sun tabbatar da haka a sakamakon da wakilan jam’iyyarsu na sassan suka gabatar masu, inda ya buƙaci ‘yan Najeriya da su zabi ‘yan takarar jam’iyyarsu a zaɓen gwamnoni da majalisar dokokin Jiha da za a yi a ranar 18 ga watan Maris.

1 COMMENT

Leave a Reply