No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta tabbatar da kashe masunta 29 da ‘yan ta’addar Boko Haram suka yi a jihar.

Harin wanda ya auku a ƙauyen Mukdolo da ke yankin Gamborun Ngala a jihar ya kuma yi sanadin jikkata wasu masunta guda tara.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Sani Kamilu, wanda ya tabbatar da hakan, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba 8 ga watan Maris, 2023.

A baya dai an ruwaito cewa, ‘yan ta’addan da dama da ke kan babura sun abka cikin filin suna harbe-harbe ba da dadewa ba, yayin da suka kewaye sauran mutane 29 da aka kashe da bindiga bayan da mutane tara suka tsere da raunuka.

KU KUMA KARANTA: Boko haram sun kai hari ƙauyen Borno, sun ƙona runbunan abinci da gidaje

Wata majiya ta shaida wa kafar yada labarai ta yanar gizo, Zagazola Makama, cewa maharan sun yi amfani da gidajen kamun kifi wajen nade masuntan, inda suka azabtar da su sannan suka buɗe musu wuta.

“Sun ce su kwanta. Bayan haka, sun yi amfani da ragarsu na kamun kifi suka naɗe su kafin su fara azabtar da su. Bayan sun suma ne sai suka bude musu wuta, inda nan take suka kashe su,” inji majiyar.

Daga baya an tsinto gawarwakin manoman a wani samame da sojojin da suka samu labarin daga waɗanda harin ya rutsa da su suka tsere daga inda aka kai harin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...