Ba zan sauka ba, shugaban INEC ga jam’iyyun adawa

0
206

Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban jukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ya ce kiran da jam’iyyar Labour (LP) da PDP suka yi na yayi murabus bai dace ba.

Rahotanni sun nuna yadda wasu jam’iyyu suka ce sun rasa kwarin gwiwar gudanar da zaɓukan da ake yi kan rashin amfani da na’urar tantance sakamakon zaɓe kamar yadda dokar zaɓe ta tanada.

A wani taron tattaunawa a Abuja, da jam’iyyun adawa suka yi, sun yi zargin cewa an yi magudi a zaɓen na ranar Asabar.

Amma da yake mayar da martani ta bakin Rotimi Oyekanmi, babban sakataren yaɗa labaransa, shugaban hukumar ta INEC, ya ce saɓanin raɗe-raɗin da jam’iyyun biyu suka yi, sakamakon da ke fitowa daga Jihohin na nuni da tsari na gaskiya da gaskiya.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sa kai sun maye gurbin ma’aikatan INEC da suka gaza zuwa aiki, a Anambra

Hukumar ta kuma ce zargin da sanata Dino Melaye ya yi na cewa shugaban INEC ya bai wa jam’iyyu maki ba gaskiya ba ne kuma bai dace ba.

“Tabbas, waɗanda suka fusata suna da ‘yanci su tunkari kotuna domin su bayyana damuwarsu, su kuma jira a warware matsalar.

“Yin tsokaci da zai iya haifar da tashin hankali ba abu ne da za a yarda da shi ba.

“Tsarin zaɓen 2023 yana kan matakin ƙarshe na kammalawa, yana da kyau waɗanda suka yi korafin su ba da damar kammala aikin kuma su tunkari kotuna da hujjojinsu don ci gaba da shari’arsu.

“Akwai tsare-tsare da aka gindaya wa jam’iyyu ko ’yan takara masu cin zarafi da za su bi idan ba su gamsu da sakamakon zaɓe ba, irin waɗannan hanyoyin ba su haɗa da yin kira ga shugaban INEC ya yi murabus ko a soke zaɓen ba.” in ji shi.

Leave a Reply