No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wata matar aure a ƙaramar hukumar Bwari ta babban birnin tarayya Abuja, ta maka mijinta ƙara a wata kotun yankin da suke zama saboda rashin gamsuwar aure daga mijinta.

Matar mai suna Baraka Abdullahi mai shekaru 23, ta zargi mijinta Bello Abdullahi da rashin zama tare da ita, da kuma rashin jin daɗin zaman aure a lokacin da ya ziyarce ta.

Matar ta shaida wa kotun cewa bayan aurensu kimanin shekaru biyu da suka wuce, mijin nata ya kai ta jiharsa ta Kano, ya bar ta a can karkashin kulawar iyayensa, yayin da ya ci gaba da zama a Abuja inda yake sana’a.

KU KUMA KARANTA:Wani Mutum da ya saki matar shi ya nemi kotu ta bashi daman shafa nononta a duk ƙarshen mako

Ta yi korafin cewa mijin da ke da wata mata a gida ɗaya da ita ya kan ziyarce su bayan kusan watanni uku ba ya nan. Ta lura cewa duk da cewa ya biya mata dukkan bukatunta na ciyar da ita, amma ta ce mijin bai taɓa gamsar da ita ba idan aka zo batun kwanciya, don haka tana bukatar saki.

Wanda ake karan ya amince ya dade da zama saboda yanayin kasuwancinsa, wanda a cewarsa, ba zai iya amincewa da wani ba, yayin da ya musanta wannan gamsuwar na aure, kuma ya zarge ta da cewa ba ta taɓa fadin haka ba.

Alkalin kotun, Abdurrahman Ibrahim, ya amince da bukatar mijin na neman a yi sulhu ta hanyar keɓe kwanaki 10 yayin da ya ɗage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...