No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wata ‘yar kasar Amurka mai suna Vonapolouis Moss, ta bayyana wa rundunar ‘yan sandan jihar Kwara yadda wani ɗan damfara yanar gizo mai shekaru 23 da haihuwa, ya yaudare ta har ta yi bulaguro zuwa Najeriya.

Ba Amurkiyar da ke zaune a gida mai lamba 2962, W 64th Court, Meryrillville, Indiana 46410 a Amurka ta ce wanda ake zargin ya yaudare ta zuwa Najeriya ne a ranar 9 ga Janairun 2023.

Wanda ake zargin ɗan damfara ne na yanar gizo da aka fi sani da ɗan yahoo, kuma ya damfari matar dubban dalolin Amurka kafin daga bisani ya yaudare ta zuwa Najeriya.

KU KUMA KARANTA:Yadda ‘yan yahoo suka yi garkuwa da abokin ta’asarsu kan kuɗin damfara

“Mun haɗu ne a dandalin tiktok inda ya gayyace ni zuwa Najeriya amma da na zo sai ya kai ni wajen ‘yan canjin kuɗi domin in canza kuɗin na dalar Amurka zuwa naira, kuma ya kai ni ShopRite muka ci abinci.

“Lokacin da kuɗin da ya ƙare, sai ya ce in gaya wa mutanena su ƙara turo kuɗi,” kamar yadda ta shaida wa ‘yan sanda yayin da ake yi musu tambayoyi.

Baturiyar ta ce tana son Najeriya amma ta fi son komawa Amurka.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...