Ƙabilar dutsen da ke ɓoye a Ƙasar Papua

0
433

Ƙabilar dutsen da ke ɓoye a ƙasar Papua, in da mazauna ƙauyen suke yi wa kakanninsu hayaƙi kuma sun ajiye gawarwakinsu a cikin wani yanayi na kusan ɗaruruwan shekaru.

An ɗauki hoton wannan basaraken na ƙabilar Dani ɗauke da gawar kakansa da aka yi wa hayaki aka ajiye.

Eli Mabel, ya na riƙe da gawar Agat Mamete Mabel a ƙauyen Wogi da ke Wamena a yammacin Papua.

Ƙabilar ƴan asalin su na zama a wani yanki mai nisa na tsaunukan tsakiyar Papuan.

Ba’amurke masanin dabbobi kuma ɗan agaji Richard Archbold ne ya gano ƙabilar a cikin shekara ta 1938.

Hotunan ban mamaki sun fito su na nuna wani basaraken ƙabila riƙe da gawar wani kakansa a wani ƙauye mai nisa na Indonesia.

Ƙabilar Dani har yanzu mutane su na adana adadin Gawarwakin a matsayin alamar girmamawa mafi girma ga kakanninsu.

A cikin ƴan shekarun nan ƴan ƙabilar Dani sun jawo hankalin ƴan yawon buɗe ido daga sassa daban-daban na duniya, inda wasu ƙauyukan suka nuna al’adunsu na asali.

A kowace watan Agusta, ƴan ƙabilar Dani na yin fadɗace-faɗace da ƙabilun da ke maƙwabtaka da su, irinsu ƙabilar Lani da Yali saboda murnar samun haihuwa.

Leave a Reply