Yadda aka yi wa ‘yar fim fashi a Landan

1
243

Fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Chita Agwu, ta bayyana cewa an sace mata kayanta masu daraja a tashar Finchley Road dake birnin Landan.

Wannan dai na zuwa ne ‘yan makwanni bayan da wasu fitattun jaruman suka yi magana game da haɗuwar su da ‘yan fashi da makami a Landan. Hakanan, Gwamnatin Tarayya ta gargadi ‘yan Najeriya game da ƙaruwar yiwuwar yin fashi a Burtaniya da Amurka.

Jarumar ta bayyana hakan ne a shafin ta na Instagram a ranar Alhamis awani sako da ta wallafa inda ta rubuta cewa, “Ya Allah! Me wannan duniyar ta zama? Ta yaya mutum zai yi barci idon sa biyu a rufe cikin dare, ya sani sarai cewa ya yi wa wani sata?

“An yi min sata a Landan, a tashar Finchley Road. Duk kayana masu daraja a cikin jaka sun tafi. “Na ɗauka mafarki nake yi, ba lafiya, na kasa yin barci jiya da daddare.” in ji jarumar.

1 COMMENT

Leave a Reply