Yadda jami’an DSS suka harbe matashi a taron siyasa a Gombe

Jami’in hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ya harbe wani matashi mai suna Auwal Hassan dan shekaru 30 a duniya, a wani gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a ranar lahadi a garin Bojude da ke ƙaramar hukumar Kwami a jihar Gombe.

Wanda aka harba, ya bi sahun sauran mutanen ƙauyen, inda suka fito domin karɓar tawagar yakin neman zaɓen Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.

Shaidun gani da ido sun shaida wa jaridar Dailytrust cewa, bindigar jami’an DSS ta bindige Hassan a kafarsa a yayin da ake ta hayaniya bayan da ayarin motocin gwamnan suka isa wurin da ake gudanar da yaƙin neman zaɓen.

KU KUMA KARANTA:Zaben 2023: an buƙaci ‘yan siyasa da gujewa yin amfani da ƙananan yara yayin gangamin siyasa

Rahotanni sun bayyana cewa wanda aka harba ɗin ya faɗi ƙasa, yana jin zafin harbin da aka mishi, lamarin da ya harzuka wasu matasan da suka fara cewa “Ba mayi” (ba ma goyon bayan ku) a wajen taron yakin neman zaɓen.

Sauran jami’an tsaron tawagar gwamnan sun yi kokarin kwantar da hankalin matasan da suka fara hayaniya.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan faruwar lamarin, Gwamna Yahaya na Gombe ya bada umarnin a kamo jami’an DSS domin gudanar da bincike cikin gaggawa.

Ya kuma bayar da umarnin a kai wanda aka harba, zuwa asibiti domin yi masa magani da kuɗin gwamnatin jihar.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa ya naɗa wanda aka harban, tare da wasu matasa huɗu daga garin Bojude a matsayin masu taimaka masa (PA).


Comments

4 responses to “Yadda jami’an DSS suka harbe matashi a taron siyasa a Gombe”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Yadda jami’an DSS suka harbe matashi a taron siyasa a Gombe […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Yadda jami’an DSS suka harbe matashi a taron siyasa a Gombe […]

  3. […] KU KUMA KARANTA: Yadda jami’an DSS suka harbe matashi a taron siyasa a Gombe […]

  4. […] KU KUMA KARANTA: Yadda jami’an DSS suka harbe matashi a taron siyasa a Gombe […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *