Akalla Malaman Addini Mutane 100 A Arewacin Najeriya Su Ka Yi Addu’ar Samun Nasara A Zaben 2023

0
540

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

AYAYIN da ake shirin bikin ranar zaman lafiya da addu’a ta duniya na ranar 21 ga watan Yuni 2022, akalla sama da malamai dari (100) musulmi da kiristoci daga Jahohin Arewacin Najeriya sha tara (19) ne suka hadu, yayin da wasu suka gabatar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya da hadin kai a wuraren ibadarsu daban-daban a kasar nan.

Malaman sun bayyana cewa Allah ya nufe su ne da su yi magana a madadin wadanda ba za su iya yin magana da kansu ba domin bukatar dorewar zaman lafiya, fahimtar juna, hakuri da afuwa a tsakanin kungiyoyi addinai daban-daban.

Da yake bayani a garin Kaduna, Babban mai kula da cocin Christ evangelical and life intervention ministry, Fasto Yohanna Buru, ya yi bayyana cewa akwai bukatar yin hakan ranar bikin wannan shekara na bikin zaman lafiya da addu’o’i.

A cewarsa, kungiyar fastoci da ’yan uwa a fadin kasar nan wadanda suka hada da kungiyarsa ta (Peace Revival and Recounciliation Foundation of Nigeria) na da bukatar a fara gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar domin babban zabe na 2023 mai zuwa.

Acewarsa, a yayin da babban zaben shekarar 2023 ke gabatowa, dukkan masu neman kujerar Sanata, Gwamna da Shugaban kasa na bukatar addu’o’in neman tsarin Allah da nasara, don haka akwai bukatar dukkanin malaman addini su shirya addu’a ga dukkan ‘yan takara ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasarsu ba.

Ya ce “Muna addu’ar Allah ya ba su hikima ta yadda za su wakilci kowa a kasar nan ba tare da la’akari da al’adu, addini, yanki, da dai sauransu ba”

“Ya Ubangiji, ka ba shugabanninmu hikima domin su yi abin da ya fi karfin fahimtarsu. Ka taimake su su zaɓi hanyar da ta dace a lokacin da suke yanke shawara a madadin wannan al’umma.”

Ya kara da cewa ya lura da cewa a kowace shekara a ranar 21 ga Yuni, ranar tana ƙarfafa mutane na kowane addinai da dukan al’ummai da su yi addu’a ga duniya. Don haka, suna yi wa dukkan yan takarar gwamna da na shugaban kasa addu’a tare da karfafa musu gwiwa wajen neman tsarin Allah, da kariya kafin zabe, da kuma bayan babban zabe.

Sun kara da cewa suna addu’ar Allah ya sa ‘yan takara su kasance masu saurare da taushin zuciya don bunkasa ilimin ‘ya’ya mata, bunkasa ayyukan noma, inganta kiwon lafiya.

Malaman addinin, sun kuma ce suna yi wa ’yan takara addu’a don magance talauci, laifuffuka, rashin aikin yi, ‘yan fashi, garkuwa da mutane, Boko Haram, IPOP da kuma matsalolin rashin tsaro da suka shafi jihohin Arewacin Najeriya 19.

“Muna addu’ar samun karfi da kwarin gwiwa ga shugabanninmu da ‘yan takarar zabe”

Da yake mayar da martani, Malam Mohammed Sani, daya daga cikin Malaman addinin Musulunci na Kaduna ya yi kira ga Musulmi da Kirista da su rika yi wa shugabansu addu’a.

Yana mai cewa, yana da kyau kowane dan kasa ya rika marawa shugabansa baya da addu’o’i masu kyau, domin Allah ya taimake shi ya sauke nauyin da yake kansa.

Daga nan sai ya yi kira ga ‘yan siyasa da su daina amfani da ‘yan daba a lokacin yakin neman zabe.

Yayin da yake kira ga jama’a da abin da ya shafi kungiyoyi masu zaman kansu, ya buƙaci su yi addu’a don dorewar dimokradiyya, kana da wayar da kan jama’a kan hanyoyin gudanar da sahihin zabe.

Dole ne a tuna cewa a cikin shekarar 1996, Cif Arvol Looking Horse ya fara gudanar da Ranar Aminci da Addu’a ta Duniya na shekara-shekara a lokacin bazarar solstice.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here