Shugaban Kungiyar Masu Sana’ar Gwari Ya Mika Sakon Ban Gajiya Ga ‘Ya’yan Kungiyar

0
329

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

SHUGABAN kwamitin riko na Kungiyar masu sana’ar Kayan Gwari na Jihar Kano, Alhaji Usman B. Dan-Gwari ya mika sakon ban gajiya ga yayan kungiyar bisa halartar daurin auren yarsa da aka yi ranar Asabar din data gabata.

Sannan ya yi godiya ga mambobin kungiyar wadanda suka halarci daurin auren wadanda suka je daga dukkanin Jihohin kasarnan duk da irin harkokin dake gaban su domin shaida wannan biki wanda hakan ya tabbatar da cewa masu sana’ar Gwari mutane ne masu hadin kai da kaunar juna.

Haka kuma Usman B. Dangwari, ya bayyana cewa zai ci gaba da aiki domin hada kan masu sana’ar gwari na jihar Kano tare da bunkasa Kungiyar a matsayinsa na shugaban kwamitin riko na kungiyar ta yadda dukkanin yan kungiyar zasu sami ci gaba mai albarka rani da damina.

Bugu da kari, Shugaba Usman B. ya bukaci gwamnatocin kasarnan da su kara kokari wajen bullo da karin hanyoyi na inganta noma da sarrafa kayan gwari domin ganin manoma da masu sarrafa kayan amfanin gona suna samun ribar wannan sana’a ba tare da gamuwa da asara ba.

A karshe, shugaban kwamitin riko na kungiyar yan gwari na jihar Kano, Alhaji Usman B. Dangwari ya yi addu’ar ci gaba da samun dawamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan kasa da duniya baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here