Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.
A KOKARIN da kungiyar koyawa jama’ a Noman zamani ta kasa wato National Agricultural Mechanization Cooperative Society (NAMCON) ke yi domin bunkasa tattalin arzikin kasa, kungiyar ta kaddamar da shugabannin ta da za su rike ragamar al’amuran a Jihar Kaduna.
Kamar yadda shugaban (NAMCON) na kasa, Dokta Aliyu Muhammad Waziri ya bayyana wa dimbin jama’ar da suka taru a wurin taron da aka yi a Kaduna cewa, su na kokarin kara bunkasa tattalin arzikin al’umma ne ta fuskar Noma da sana’o’i.
Aliyu Waziri wanda shi ne Santurakin Tudun Wada Kaduna, ya kara da cewa akwai wadansu tsare-tsare guda biyar da suke kira da cewa muhimman Kudirori biyar da kungiyar Noman zamani (NAMCON) ta mayar da hankali a kansu.
Da yake bayanin irin hanyar da ake samar da wadanda za su yi wannan horaswa, ya bayyana cewa akwai hanyar yin rajista da kowa ce karamar hukuma za ta yi wa mutane 20 rajista kuma duk wanda ya yi rajista zai biya kudi naira dubu sittin da shida.
Ya kuma ce wadanda za su yi aikin kula da Kajin kowa zai yi rajista a kan kudi naira dubu Hamsin da biyar da za a yi masu taron bayar da horo na tsawon wata daya kuma abinci da duk dawainiya ita ce na wannan kudin.
Dokta Aliyu Muhammad Waziri, ya tabbatar wa da dimbin al’ummar da suka halarci taron cewa a halin yanzu an gudanar da irin wannan taro na kaddamar da shugabannin Jiha da na shiyyoyin Jiha kuma yan ciye ciye da tande- tanden da za a yi a wurin bayar da horon da kuma Kajin da za a kawo wurin bayar da horon da kuma bayar da takardar shedar kammala taron duk a cikin kudin da suka bayar ne.
Sannan ita wannan takardar shedar kammala horo ta nuna cewa kuma da akwai kamfanin Inshora domin maganin duk wata maganar yin asara da dai ba a fatar hakan.
Shugaban kungiyar na Jihar Kaduna, Alhaji Sanusi Abdullahi Abubakar, cewa ya yi a duk fadin Najeriya, Jihar kaduna ce a kan gaba dangane da batun kungiyar (NAMCON) kasancewar a Jihar ne aka kirkiri kungiyar da a yanzu ta karade kasa baki daya.
Ya ce “Saboda haka muna yi wa jama’a albishirin cewa za a samu gagarumin ci gaban da kowa zai amfana a ciki da wajen Najeriya baki daya.”
“An kafa wannan al’amari ne domin a Koyar da mata su samu arziki musamman idan an koya masu kiwon Kaji da sauran sana’o’i da nufin bunkasa tattalin arzikin kasa.’
Sanusi Abdullahi, ya kuma yi bayanin cewa dalilin da yasa suka karkata ga mata shi ne kasancewarsu a matsayin Jigon gida baki daya, don haka idan ka karfafa tattalin arzikinsu, hakika za a samu ci gaba mai alkairi a cikin jama’a.
Abubuwa biyar da za a yi karkashin wannan kungiya shi ne, Koyar da kiwon Kaji na zamani da za a tallafa wa mata da suke a cikin gidaje.
Kuma za a gina masu Gidajen da za su rika yin kiwon Kajin a ciki, za kuma a samu masu kiwon Kaji Mata, za a samu wadanda za su rika kula da Kajin Ashirin da Safe, Ashirin da Yamma.
Sai kuma wadanda suke da ilimin likitancin Dabbobi, wannan kungiyar ita za ta bayar da abinci da magani da masu kula wa da sa idanu su ga cewa Kajin ana ba su abinci da magani da nufin su samu ingantacciyar lafiya.
“Wannan kungiyar na da wurin da za ta sayar da Kajin ta idan lokaci ya yi, saboda haka ita shugabar wurin kiwon Kajin za a ba ta kudi naira dubu dari da Hamsin, sannan su wadanda ke kula wa da Kajin za a ba kowane dubu Hamsin da Biyar. Za kuma a dinga yinsa duk bayan Sati shida da nufin nan da shekaru biyu duk abin da ya shafi Kaji da Kiwonsu kuma za a tabbatar cewa wadanda aka horar da wadanda suke shugabanci da kula da kiwon Kajin sun fahimci komai, kuma kudin da ake ba su za su iya ajiye wani abu daga ciki ya kasance sun samu jari wanda daga baya su san me za su yi kuma ruwansu ne su yi rajista ko su fice daga kungiyar kasance sun iya sana’ar da za su zauna da kansu a koda yaushe.