DSS Ta Tsare Alfindiki, Murtala Sule Garo, Alhassan Ado Doguwa

0
385

Daga; Rabo Haladu.

HUKUMAR tsaron farin kaya na cikin gida wato (DSS) ta tsare wasu manyan na hannun-daman gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Bayanan da manema labarai suka samu sun nuna cewa DSS ta tsare mutanen ne ranar Laraba bisa zarginsu da hannu a dabar-siyasa.

Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jihar ta Kano, Murtala Sule Garo, wanda ya tabbatar da wannan labarin, ya ce yana cikin manyan Jami’an Gwamnatin Jihar da suka mika kansu ga DSS.

Sauran mutanen sun hada da Fa’izu Alfindiki, shugaban karamar hukumar Birnin Kano, Khalid Ishaq Diso, shugaban karamar hukumar Gwale da Injiniya Bashir Kutama, shugaban karamar hukumar Gwarzo.

Murtala Garo ya ce an gayyaci mutumin da ke son Jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar gwamnan Jihar ta Kano a zaben 2023, A.A Zaura, da shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa, da shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan Agundi, da kuma wani mai bai wa Gwamna shawara.

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin wasu daga cikinsu da hannu a manyan-manyan hare-haren dabba, lamuran da suka yi sanadin mutuwar wasu mutane.

A baya bayan nan dai ‘yan siyasa musamman na Jam’iyyar APC sun rika sukar juna bayan raba gari tsakanin bangaren Gwamna Ganduje da tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau, sai dai tun kafin hakan an rika jifan juna da muggan kalamai da kuma amfani da ‘yan daba domin biyan bukatu na siyasa.

Wancan lokaci ne yanayin siyasa ya kara yin zafi tsakanin bangaren Murtala Sule Garo da kuma Sanata Barau Jibrin, wanda shi ma ake rade-radin yana son tsayawa takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here