Rikicin APC: Ɓangaren Shekarau Ya Yi Fatali Da Sulhun Uwar Jam’iyyar Kan Rikicin Kano

0
395

Daga Wakilinmu

Rikicin shugabancin jam’iyyar APC a Kano na ƙara daukar sabon salo bayan ɓangaren da Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta ya yi watsi da sanarwar uwar jam’iyya kan sulhunta rikicin ‘ya’yanta na jihar.

Matsayar tsagin Sanata Shekarau da ya zabi Alhaji Haruna Dan-Zago a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar Kano na da alaƙa da bai wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje jagorancin kwamitin da zai warware matsalar.

A wata hira da BBC ta yi jim kadan bayan fitowar sanarwar jam’iyyar APC ta kasa, Sanata Ibrahim Shekarau ya ce sun yi watsi da wannan sanarwa kuma ba su amince da ita ba.

Ganduje da Shekarau

”Matsayinmu akan wannan sanarwa matakai ne kamar guda uku: a duk zaman da muka yi kamar sau biyu ko sau uku, wanda mai girma gwamna Ganduje ya na wurin da mukarrabansa da wadanda mu ma muka je tare da su, karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar gwamnan jihar Yobe Maimala Buni.

An nemi kowanne ɓangare ya bayyana matsayarsa da abin da suke son a yi da shawarar waraka kan wannan matsala, dukka mun bayar da na mu. Shugaban jam’iyya ya ce za su koma su kalli bayanan da dukka muka yi domin fito da wata mnatsaya, da shawarar abin da ya dace a yi.”

Sanata Shekarau ya kara da cewa, sanarwar da jam’iyyar APC ta fitar ba ta yi magana a kan matsayar da aka cimma tsakanin ɓangarorin biyu ba, sannan jam’iyya ba ta fadi komai tsakanin abin da ɓangarorin biyu suka bukata ba.

Abu na biyu kafin a kawo takardar a matsayin wanda ya ke jagorantar ɗaya bangaren, sai da aka kai wa gwamna Ganduje takardar wadda kamata ya yi ta zama tsakanin shugaban jam’iyyar, ko hedikwatar jam’iyya, da gwamna da kuma ni shugaban ɗayan barin jam’iyyar, in ji Shekarau

Sannan ya ci gaba da cewa kafin su samu takardar ta shiga duniya tana yawo a shafukan sada zumunta.

“Yaran gwamna na cewa an danƙawa gwamna jam’iyya ai ta koma hannunsa da maganganu makamantan haka.

“Abu na uku shi ne ya ya mutane biyu su na jayayya, sai kuma a ce ɗaya daga cikin wadanda ake jayayya da shi ne zai jagoranci sasantawar, alhalin shi ya jagoranci waccan sasantawar da ba a yi mana adalci ba, da muke ganin an zalunce mu, ta ya ya za a yi mana adalci a yanzu.”

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kamata ya yi uwar jam’iyya ta wakilta wanda zai jagoranci wannan zama. Don haka ba mu amince da shi ba, mun yi fatali da shi, ba mu yadda ba, ba kuma za mu amince ba, a karshen takardarmu mun fadawa uwar jam’iyya mu masu biyayya ne, a shirye muke a sake zama domin sasantawa,” in ji Shekarau.

Shekarau ya ce wannan dalili ya sa suka rubuta takarda suka aikawa shugaban jam’iyya, za kuma su bai wa ‘yan jarida da shafukan sada zumunta cewa abin da sukayi tsammani a yi ba shi aka yi ba.

A daren Litinin ne uwar jam’iyyar ta fitar da sanarwa kan yadda za a shawo kan matsalarsu da magance ta.

Ta kafa kwamitin mutum biyar domin warware rikicin shugabanci da ya ki ci ya ki cinyewa a jihar Kano da ke arewacin ƙasar tsakanin ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau da na gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Jam’iyyar ta sanya gwamna Ganduje a matsayin shugaban kwamitin, sai kuma Sanata malam Ibrahim Shekarau a matsayin mataimakinsa.

Dukkan mutanen biyu dai na ja-in-ja kan shugabancin jam’iayar APC a jihar ta Kano, lamarin da ya janyo takun saka da sanya jam’iyyar cikin halin kaka-ni-kayi a jihar.

Sauran ‘yan kwamitin akwai gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle, da tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, da Sanata Abba Ali, da kuma wakilin jam’iyyar da ke sa ran za a yi zama da shi.

Sanarwar ta kuma ci gaba da cewa ana san kwamitin zai yi zama a jihar Kano cikin kwanaki bakwai tare da miƙawa jam’iyyar rahoto.

Sannan ta na fatan bai wa gwamna Ganduje shugabancin kwamitin a matsayinsa na kamar shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano zai nuna kyakkyawan shugabanci a zaman da za a yi.

APC ta ce an dauki matakin ne saboda kotu ta gagara warware rikicin, alhalin dukkan bangarorin biyu ba za su kai labari ba a lokacin zabe dole sai da dan uwansa.

Sanarwar ta kara da cewa, domin samun warware matsalar da samun jam’iyya guda ba kungiya-kungiya a jihar ta Kano, ya na da matukar muhimmanci gwamna Ganduje ya jagoranci kwamitin.

Haka kuma, adalcin anan ba wai rarraba madafun iko na jam’iyyar kadai ba ne, har da yi wa sauran ‘yan jam’iyyar adalci ta fuskar shugabanci.

Kano dai babbar jiha ce da APC ta daɗe tana nanata tasirinta a siyasar Najeriya, abin da yasa APCn ke ƙara ƙoƙari wajen ganin ta hana wannan ɓaraka da ta kunno kai a jihar ƙara tsawo da faɗi.

Idan aka gaggara maslaha tun da wuri babu mamaki wannan rikici ya kassara tasirin da APCn za ta iya yi nan gaba.

Kodayake ‘ya’yan jami’iyyar na da kwarin-gwiwar sulhu zai tabbatu a tsakaninsu.

Leave a Reply