No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Rabo Haladu

Rundunar ƴan sandan ta musanta rahotannin da wasu kafofin yaɗa labaran ke cewa wani jirgi mai saukar ungulu mallakarta ya yi hatsari a Bauchi.

Rundunar ta kuma musanta labaran da ke cewa waɗanda suke cikin jirgin sun samu munanan raunuka.

Rundunar ta ce jirgin wanda ya taso daga Abuja a ranar 26 ga watan Janairun 2022 ya yi saukar gaggawa ne a filin jirgin sama na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Rundunar ta ce duka mutane shida da ke cikin jirgin lafiyarsu kalau haka kuma rundunar ta ce direban jirgin ƙwararre ne wanda a dalilin haka ne ya sa ya sauka lafiya ba tare da jirgin ya yi dameji sosai ba.

Rundunar ta ce farfelar jirgin ta baya ce kawai ta samu matsala a yayin sauka.

Tun da farko dai gidan rediyon  tarayyar  ya ruwaito Hukumar Binciken Haɗurran Jiragen Sama ta ƙasar, AIB tana tabbatar da labarin.

admin
adminhttps://neptuneprimehausa.com
Ni ɗan jarida ne mai zaman kansa. Mawallafi kuma mai sharhi a lamarin yau da kullum.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...