Mu’azu Magaji: ‘Yan Sanda Sun Kama Tsohon Kwamishinan Ayyuka Na Kano

0
287

Daga Wakilinmu

Wasu ‘yan sanda a Abuja, babban birnin Najeriya sun kama tsohon Kwamishinan Ayyuka na jihar Kano, Mu’azu Magaji.

Lauyansa da kuma iyalansa sun tabbatar wa Wakilinmu cewa an kama tsohon Kwamishinan ne ranar Alhamis da daddare lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa masaukinsa bayan ya gama harkokinsa na ranar.

Lauyansa, Barrister Garzali Datti Ahmad, ya shaida wa BBC Hausa cewa suna zargin gwamnatin Kano ce ta tura ‘yan sanda Abuja suka kama shi.

Mu’azu Magaji, wanda ake yi wa lakabi da Ɗan Sarauniya, ya dade yana sukar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje tun ma kafin a sauke shi daga kan mukaminsa.

Leave a Reply