Me ya hana Sanata Natasha dawo wa majalisa, bayan lokacin dakatarwar da aka mata ya ƙare?
Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta ce Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ba za ta iya komawa ofis ba duk da cikar watanni 6 da aka dakatar da ita.
Sanatar Kogi ta Tsakiya ta rubuta wa Majalisar Dokoki ta Ƙasa tana sanar da su cewa wa’adin dakatarwar ta ƙare, tare da bayyana niyyarta ta komawa majalisar dattawa.
Sai dai duk da cewa majalisar na hutu a halin yanzu, sakataren majalisar ya mayar da martani yana cewa dakatarwar da ta fara aiki tun ranar 6 ga Maris, 2025 har yanzu na gaban kotu.
A cewar wasikar da gidan talabijin na AIT ya gani, sai an kammala shari’ar sannan majalisar ta duba hukuncin kotu kafin a iya ɗaukar wani mataki.
KU KUMA KARANTA: Dole a binciki zargin lalata da Natasha ta yiwa Akpabio – Amnesty
A wani ɓangare na wasikar da mai rikon mukamin sakataren majalisar, Yahaya Danzaria ya sanya wa hannu, ya ce:
“Batun dakatarwarki na gaban Kotun Daukaka Kara a halin yanzu. Saboda haka, sai an kammala shari’ar sannan majalisar dattawa ta sake duba dakatarwar bisa ga hukuncin kotu, kafin wannan ofishi ya ɗauki matakin gudanarwa don ba ki damar komawa. Za ki samu sanarwa kan hukuncin majalisar dattawa idan an kammala batun.”
A baya, Sanata Natasha ta yi ƙoƙarin komawa aiki ranar 12 ga Yuli, bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta umurci majalisar dattawa da ta sake duba dakatarwar. Amma aka hana ta shiga harabar majalisar.
Sanatar da kuma Majalisar Dokoki ta Ƙasa duka sun ɗaukaka ƙarar ɓangaren hukuncin, wanda yanzu haka ke jiran sauraro a gaban Kotun Daukaka Kara.








