Ɗan yawon buɗe ido na Amurka ya mutu bayan faɗowa daga Rufin otal mai tsayi 100

1
335

Wani ɗan yawon buɗe ido ɗan ƙasar Amurka da ya ziyarci birnin Rome na ƙasar Italiya ya gamu da ajalinsa bayan ya hau rufin otal mai hawa 100 da ke babban birnin Italiya, ya kuma duro, kamar yadda jami’ai birnin suka bayyana.

A cewar jaridar Daily Mail ranar Juma’a, ɗan yawon buɗe idon mai suna Javier Francisco Rullan Rubert, mai shekaru 31, ya fito daga yankin Florida, ya kasance a Otal din IH Roma Z3 da ke Collatino a Rome, na tsawon kwanaki inda yake hutu.

A ranar Litinin da yamma, da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, ma’aikatan otal suka same shi kwance a kasa cikin jini bayan ya fado daga saman rufin Otal ɗin.

KU KUMA KARANTA: Matsirga Waterfalls, Kaduna, Najeriya

Jami’an ‘yan sanda masu binciken ƙwaƙwaf sun fara gudanar da bincike wanda ya ƙunshi sake gina kwanakin ƙarshe na mutumin da kuma kafa duk wata alaƙa da ya yi a lokacin.

Wasu daga cikin kayayyakin mutumin da suka haɗa da wayar salula, jami’an suna riƙe da su domin tantance su.

Mutumin bai bar wa ’yan uwa da abokan arziki bayaninsa ko wata wasiyya ba, don haka jami’ai suna ta kai komo don tuntubar ’yan uwansa don sanin yadda ainihin abun da ya kai ga mutuwarsa.

A cewar kafar yaɗa labarai ta The Italian Insider, masu binciken suna jingina mutuwara akan kashe kansa amma ba su kawar da wasu hasashe da basu da alaƙa da hakan ba.

1 COMMENT

Leave a Reply