Ɗan ƙunar-baƙin-wake ya kashe mutane 52 a wurin Maulidi a Pakistan

0
253

Daga Ibraheem El-Tafseer

Lamarin ya faru a ranar Juma’a da safe kuma jami’an lafiya sun ce sama da mutum 50 sun jikkata sakamakon harin. Babu ƙungiyar da ta ɗauki nauyin kai wannan hari zuwa yanzu.

A ƙalla mutane 52 ne suka mutu sannan sama da 50 suka jikkata sakamakon wani harin ƙunar baƙin-wake da aka kai a taron Maulidi a lardin Balochistan na Pakistan, kamar yadda jami’an lafiya da ‘yan sanda suka tabbatar.

Babu wata ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai harin wanda yake zuwa a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-hare a yammacin ƙasar.

“Ɗan ƙunar-baƙin-waken ya tayar da bam ɗin ne kusa da motar mataimakin sufuritanda na ‘yan sanda,” kamar yadda Babban Sufeto Janar na ‘yan sanda Munir Ahmed ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

KU KUMA KARANTA: Harin ƙunar baƙin wake a Somaliya ya kashe sojoji 13

Ya ƙara da cewa an samu tashin bam ɗin ne kusa da wani masallaci wanda mutane ke taruwa domin bikin Maulidi, wadda rana ce ta hutu.

Ƙungiyar Tehrik-e Taliban Pakistan mai iƙirarin jihadi ta musanta kai wannan hari.

Ana yi wa waɗanda suka jikkata magani a wani asibiti da ke garin Mastung wanda ke kusa da inda lamarin ya faru.

A watan Yuli, sama da mutum 40 ne suka rasu a harin ƙunar-baƙin-wake a arewa maso yammacin lardin Khyber Pakhtunkhwa a yayin wani taron addini.

Ana yin taron maulidi ne domin murna da zagoyowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW), inda miliyoyin al’ummar musulmi suke gudanar wa a faɗin duniya.

Leave a Reply