Ɗalibar jami’ar Abuja da ta ɓace ranar Juma’a, ta rasu

0
147

Iyayen wata ɗalibar aji huɗu aa Jami’ar Abuja, Murjanatu Zubairu, da ta ɓace ranar Juma’a, sun ce ta mutu. 

Kawun marigayiyar, Alhaji Zubairu Jibrin Yewuti ne ya tabbatar wa wakilin mu da rasuwarta a ranar Litinin.

Ya ce iyayen Murjanatu sun  sanar da shi cewa bayan gudanar da bincike mai zurfi sun gano cewa ta rasu ne a wani mummunan hatsarin mota a yammacin ranar Juma’a a kan hanyar Lugbe.

A cewarsa, iyayen yarinyar sun gano gawarta ne a dakin ajiye gawarwaki na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada lokacin da suka je asibitin domin tambayar ko an kawo ta ba lafiya ko wani abu makamancin haka.

KU KUMA KARANTA: Mutum 3 sun rasu, an jikkata 10 a rikicin sojoji da ’yan Keke NAPEP a Yobe

Alhaji Zubairu ya ce, “iyayenta sun ƙira ni sun sanar da ni cewa ta rasu ne a hatsarin mota da ya rutsa da ita a babban titin Lugbe zuwa filin jirgin Abuja.”

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) na shiyyar Lugbe, Sunday Ajokotola, ya tabbatar da cewa mutane 10 ne hatsarin mota ya rutsa da su, inda mace ɗaya da maza uku suka ƙone ƙurmus a ranar Juma’ar da ta gabata.

Leave a Reply