Ƴan Daba sun kai hari Ofishin Civil Defence da ke Unguwar Samegu a Kano

0
161
Ƴan Daba sun kai hari Ofishin Civil Defence da ke Unguwar Samegu a Kano

Ƴan Daba sun kai hari Ofishin Civil Defence da ke Unguwar Samegu a Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Wasu yan daba sun kai hari ofishin jamiʼan hukumar Civil Defence da ke Samegu a Karamar Hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

Kakakin Hukumar a Kano SC Ibrahim Idris Abdullahi ne ya tabbatar da hakan.

KU KUMA KARANTA:Yan Daba sun shiga gidansu wani matashi sun kashe shi a Jihar Kano

Ya ce, harin ya biyo bayan korafin wani mai kwacen waya da yan Bijilanti suka kai musu, don haka yan dabar suka je mayar da martani.

Wasu rahotonni da Jaridar Neptune Prime Hausa ta samu sun tabbatar da cewa an samu raunuka har ma ana fargaba akwai asarar rai.

Leave a Reply