Ƙungiyar da ke da alaƙa da Al-Qa’ida ta yi iƙirarin yin garkuwa da wasu ‘yan ƙasar Rasha 2 a Nijar

0
30
Ƙungiyar da ke da alaƙa da Al-Qa'ida ta yi iƙirarin yin garkuwa da wasu 'yan ƙasar Rasha 2 a Nijar
Link daftar PVP777
Link daftar Slot DANA

Ƙungiyar da ke da alaƙa da Al-Qa’ida ta yi iƙirarin yin garkuwa da wasu ‘yan ƙasar Rasha 2 a Nijar

Wasu mutane biyu da ke iƙirarin su ‘yan ƙasar Rasha ne kuma suka ce mayaƙan da ke da alaƙa da Al-Qa’ida sun yi garkuwa da su a Nijar, sun bayyana a wani bidiyo da aka wallafa a kafar yaɗa labaran da ke da alaƙa da ƙungiyar ta masu tsattsauran ra’ayi.

Bidiyon, wanda ya bayyana a kafar yaɗa labaran az-Zallaqa a daren Juma’a, ya nuna wasu mutane biyu da suka ce mayaƙan sun kama su a lokacin da suke aiki a Baga da ke arewa maso gabashin Nijar.

Mazan guda biyu, sun yi magana a cikin a bidiyon. Ɗaya daga cikinsu ya bayyana kansa a matsayin Yury, yana mai cewa shi masanin ilimin yanayin ƙasa ne kuma yana aiki da wani kamfanin ƙasar Rasha a lokacin da ‘yan mayaƙan kungiyar JNIM masu alaƙa da Al-Qa’ida a yankin suka kama shi. Ɗayan mutumin shi ma ya bayyana sunansa, amma ba iya jin shi ba sosai, ya ce ya yi wata guda a Nijar.

Kamfanin dillancin labaran AP bai iya tantance sahihancin bidiyon ba da kuma lokacin da aka ɗauke shi. Mutanen da suka yi magana da harshen turanci, ba su bayyana lokacin da aka kama su ba.

KU KUMA KARANTA:Shugaba Tiani na Nijar ya zargi Faransa da son tada zaune tsaye a ƙasar

Wata majiyar tsaro a Nijar da ta nemi a sakaya ta, ta ce kusan mako guda kenan da aka sace mutanen biyu a yayin da suka kai ziyara wata mahaƙar zinare.

Wannan ne karon farko da aka ga mutanen. Idan zancen ya tabbata, to sun zama ‘yan Rasha na farko da mayaƙan jihadi suka yi garkuwa da su a yankin Sahel, duk da kasancewar sojojin Rasha a yankin.

Yayin da dangantaka tsakanin ƙasashen yammacin duniya da ƙasashen da sojoji suka yi juyin mulki a yankin kudu da hamadar Sahara ke taɓarɓarewar, Rasha na amfani da wannan damar ta tura mayaƙanta da kuma ƙarfafa tasirinta a yankin.

A ‘yan watannin baya-bayan nan Nijar ta janye daga abokan hulɗarta na yammacin duniya musamman Faransa da Amurka, a maimakonsu ta rungumi Rasha domin samar da tsaro. A cikin watan Afrilu, masu horar da sojoji na Rasha suka isa Nijar don ƙarfafa matakan tsaron Nijar ta sama.

Wannan bidiyon dai na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da ƙungiyar Al-Qa’ida ta yi iƙirarin kai hari mafi muni kan sojojin hayar ƙungiyar Wagner na Rasha a shekarun baya-bayan nan, a lokacin da ta yi wa mayaƙan kwantan ɓauna a Mali har ta kashe sojoji 50.

Nan take dai ma’aikatar harkokin wajen Rasha ba ta mayar da martani ba game da mutanen da aka yi garkuwa da su.