Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Barcelona ta sayi ɗan wasa mai shekaru 26, Dani Olmo
Daga Ali Sanni
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona dake ƙasar spaniya ta sayi ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta RB Leipzig dake tsakar Jamus akan euro miliyan 60.
Ɗan wasan, ya rattaba hannu akan kwantiragi na tsawon shekaru shida a ƙungiyar ta Barcelona.
KU KUMA KARANTA;Tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka, Issa Hayatou, ya rasu
Ƙungiyar ta Barcelona nasa ran ɗan wasan zai buga a wasan cin kofin Gamper da ƙungiyar ta Barcelona keyi kafin tunkarar sabuwar kakar wasannin.