Ƙasar Kongo za ta ƙarbi kashin farko na allurar rigakafin ƙyandar biri

0
42
Ƙasar Kongo za ta ƙarbi kashin farko na allurar rigakafin ƙyandar biri

Ƙasar Kongo za ta ƙarbi kashin farko na allurar rigakafin ƙyandar biri

Kongo za ta karɓi kashin farko na alluran rigakafin don taƙaita yaɗuwar cutar ƙyandar biri wato Mpox a mako mai zuwa daga Amurka, kamar yadda Ministan Lafiya na ƙasar ya bayyana a ranar Litinin.

Hakan na zuwa kwanaki kaɗan bayan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana ɓarkewar cutar a matsayin barazana.

An tabbatar da ɓarkewar cutar a tsakanin yara da manya a ƙasashen Afirka fiye da goma, sannan sabon nau’in ƙwayar cutar na yaɗuwa sosai, kazalika ana fama da ƙarancin alluran rigakafin cutar a nahiyar.

DRC tana da adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar Mpox, kana tana buƙatar allurar rigakafi miliyan uku a halin yanzu.

KU KUMA KARANTA: An samu ɓarkewar cutar annobar ƙyandar Biri a Najeriya

Amurka da Japan sun yi tayin bayar da gudunmawar allurar rigakafin, kamar yadda Ministan Lafiya na ƙasar Roger Kamba ya shaida wa manema labarai.

Ko da yake dai bai bayyana adadin yawan allurar ko kuma lokacin da ƙasar Japan za ta aika da nata ba.

A rahoton da Hukumar WHO ta fitar, ta ce sama da mutum 17,000 ne suka kamu da cutar sannan mutum 500 ne suka mutu sakamakon cutar a faɗin duniya a wannan shekara.

Sama da kashi 96 cikin 100 na waɗanda suka kamu da cutar da waɗanda suka mutu sun fito ne daga Kongo, ƙasar da tsarin kiwon lafiyarta ya daɗe yana fuskantar koma baya wajen daƙile ɓarkewar cututtuka a faɗin ƙasar da kuma rashin ababen more rayuwa.

Yara ‘yan ƙasa da shekaru 15 ne suka ɗauki kaso sama da 70 cikin kashi 85 na mace-macen da aka samu a Kongo, kazalika masana kimiyya sun nuna damuwarsu game da sabon nau’in cutar mpox a Kongo wanda za a iya yaɗa shi cikin sauƙi.

A makon da ya gabata, Sweden ta bayyana samun rahoton ɓullar sabon nau’in cutar a ƙasar.

Saɓanin sauran nau’in cutar Mpox na baya, inda aka fi ganin guraje a kan ƙirji da hannaye da kuma ƙafafu, sabon nau’in cutar yana haifar da ƙananan cututtuka da ƙuraje a kan al’aura.

Wannan yanayin yana da matuƙar wahalar ganewa, ma’ana mutane na iya yaɗa cutar ba tare da sun sani ba.

Ba ta iska ake ɗaukar cutar ba, yawanci dai ana buƙatar kusancin fata da fata wajen yaɗuwarta.

Hukumar ta WHO ta ce, a karon farko an gano cutar mpox ne a ƙasashen yankin gabashin Afirka huɗu da suka haɗa da Burundi da Kenya da Rwanda da kuma Uganda, sannan baki ɗaya an danganta su da ɓarkewar cutar a Kongo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here