Ƙasar Japan za ta taimaka wa mata da yara sama da dubu 3 a harkar kiwon lafiya a Yobe

0
91
Ƙasar Japan za ta taimaka wa mata da yara sama da dubu 3 a harkar kiwon lafiya a Yobe

Ƙasar Japan za ta taimaka wa mata da yara sama da dubu 3 a harkar kiwon lafiya a Yobe

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da ayyuka na musamman (UNOPS) ya miƙa aikin maido da kula da lafiyar mata da yara ga al’ummar jihar Yobe.

Taron wanda ya gudana a babban Asibitin Jakusko, tare da haɗin gwiwar ma’aikatar lafiya ta jihar Yobe da kuma ƙungiyar ci gaban Arewa Maso Gabas (NEDC) ne suka ɗauki nauyin shirya taron. Ana sa ran aikin mata sama da 300,000 ne za su ci gajiyarsa kai tsaye a faɗin jihar.

Idan dai za a iya tunawa, rikicin Boko Haram ya addabi sassan jihar Yobe a shekarun baya, wanda ya yi sanadin lalata da ɓarnata kiwon lafiya, asibitin, motoci da kashe wasu ma’aikatan lafiya.

Misalin irin waɗannan irin za a iya ganowa a watan Yunin 2022 an ƙona motocin ɗaukar lafiya, an lalata kayan aikin jinya, an sace magunguna da kayan aikin jinya a wasu ƙananan hukumomi irinsu Geidam, Yunusari, Gujba, Gulani, Tarmuwa da Bursari. Bugu da ƙari, an ƙona gine-ginen asibiti da motoci.

A wani ɓangare na ƙoƙarin da jihar ta yi, an sake gina wuraren da aka lalata tare da inganta tsare-tsare na tsaro don hana aukuwar hare-hare a kiwon lafiya a nan gaba, ta hanyar ba da kulawa ta yau da kullum ga kiwon kiwon lafiya.

KU KUMA KARANTA: Abin da ya sa ɗalibi ya fashe da kuka don ya faɗi a gasar ‘Spelling Bee’ a Yobe

Wannan aikin na gwamnatin ƙasar Japan ya samar da kiwon lafiya don isar da ingantattun kula da lafiyar mata, jarirai da yara a cikin al’ummomin da rikicin baya-bayan nan ya shafa a Yobe, musamman harin Yunin 2022.

Da take tsokaci wajen taron, shugaban UNOPS wanda ya samu ikon shugabar tsare-tsare Emily Muga ta bayyana cewa, “manufofin UNOPS ita ce kawo ci gaba ta hanyar tabbatar da cewa iyaye mata da ƙananan yara da za a samar musu da magungunan kiwon lafiya ta hanyar amfani da waɗannan kayan aikin”.

Da take amsa tambaya kan ƙalubalen da suka fuskanta, ta ce ƙalubalen farko shi ne samar da wutar lantarki saboda rashin ƙa’ida da samar da daidaitaccen ƙarfin lantarki da na’urorin ke buƙata ba.
Aikin wanda ya fara daga ranar 29 ga Fabrairu 2023 zuwa 30 ga Yuni 2024 ya mayar da hankali kan saye da nuna more rayuwa na kiwon lafiya.

A Babban Asibitin Jakusko, an gyara ɗakin aikin tiyata da gwaje-gwajen likitanci tare da samar da kayan aiki a wani ɓangare na aikin mai taken “Mayar da Agajin Gaggawa, Kula da Lafiyar Mata da Yara a Jihar Yobe” “.

Shi ma da yake magana a wajen taron, babban Jami’in Kula da Lafiya (PMO), Dakta Sani Kadugum ya godewa ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da batun yi (UNOPS’) da gwamnatin ƙasar Japan da hukumar raya arewa maso gabas (NEDC) da yankin jihar Yobe da suka da irin wannan aiki na yabawa a Jakusko, wanda zai yi tasiri kai tsaye ga rayuwa na al’umma.

Manyan jami’an gwamnatin da tarihin gwamnatin da na ƙananan yara da masu riƙe da muƙaman gargajiya da dai sauransu duk sun halarci bikin miƙa ragamar aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here