Ɗan asalin jihar Kano ya zo na 4 a musabaƙar karatun Alƙur’ani ta duniya
Daga Jameel Lawan Yakasai
Bashir Abdullahi Bature ɗan jihar Kano, wanda ya wakilci Najeriya a Musabaƙar Attibyan da aka gudanar a ƙasar Amurka ya kare a mataki na 4.
KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar mahaddata Alƙur’ani na Najeriya sun ziyarci Neptune Prime nuna goyon baya ga Tumsah
Bashir Abdullahi Bature ya samu wannan nasara ne bayan yayi karatu a bangaren Ƙira’oi guda goma.









