Ƙasar Mali ta yanke hulɗa da Ukraine kan zargin goyon bayan ‘yan ta’adda

0
84
Ƙasar Mali ta yanke hulɗa da Ukraine kan zargin goyon bayan 'yan ta'adda

Ƙasar Mali ta yanke hulɗa da Ukraine kan zargin goyon bayan ‘yan ta’adda

Mahukunta a Mali sun sanar da yanke hulɗar diflomasiyya da Ukraine bayan ƙasar ta bayyana cewa tana da hannu a wani mummunan hari da aka kai ƙasar da ke yammacin Afirka a kwanakin baya.

“Gwamnatin riƙon ƙwarya ta Jamhuriyar Mali ta yi matuƙar kaɗuwa da bayanan da kakakin hukumar leƙen asiri ta sojin Ukraine Mr. Andriy Yusov, ya yi cewa Ukraine na da hannu a mummunan hari na rashin imani da gadara da ‘yan ta’adda matsorata ska kai wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaron Mali a yankin Tinzaouaten, tare da lalata kayayyaki,” a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin Mali Kanar Abdoulaye Maiga ya fitar ranar Lahadi.

Ranar Litinin ɗin da ta gabata rundunar sojin Mali ta tabbatar da mutuwar sojoji da dama sakamakon ba-ta-kashi da dakarun ƙasar suka yi da ‘yan ta’adda a Tinzaouaten da ke arewacin ƙasar. Kazalika rundnar sojojin haya ta Rasha mai suna Wagner da ke goyon bayan sojojin Mali ta tabbatar da mutuwar mayaƙanta ciki har da wani kwamanda a ba-ta-kashin.

KU KUMA KARANTA: Majalisar Dokokin Turkiyya ta amince a aika sojojin ƙasar zuwa Somaliya tsawon shekara 2

Shi ma jakadan Ukraine a ƙasar Senegal, Yurii Pyvovarov, ya tabbatar da sa hannu dakarunsu inda kuma ya fito ƙarara ya goyi bayan ‘yan ta’addan duniya, musamman na ƙasar Mali, a cewar Maiga.

Maiga ya ce jami’an gwamnatin Ukraine sun daɓa wa cikinsu wuƙa bayan da suka fito ƙarara suka cewa “za su ƙara yin mummunan aiki.”

“Waɗannan manya-manyan zarge-zarge, da babu wanda ya musanta, sun nuna cewa jami’an gwamnatin Ukraine suna goyon bayan ta’addanci a Afirka, da yankin Sahel musamman ma a Mali,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa kalaman da Yusov da Pyvovarov suka yi “sun nuna ayyukan ta’addanci da goyon bayan ‘yan ta’adda ba tare da shakku ba.”

Don haka gwamnatin Mali ta yanke hulɗar diflomasiyya da Ukraine nan-take, kuma za ta mika lamarin gaban hukumomin shari’a da suka dace, domin su ɗauki mataki na hana ta wargaza Mali.

Maiga ya ce za su gabatar da batun ga hukumomin Afirka da na ƙasashen duniya tare da hujjojin da ke nuna cewa Ukraine tana goyon bayan ta’addanci a duniya.