Ɗaruruwan mutane sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Afghanistan — Taliban

0
82

Hukumomin Taliban sun ce an rasa rayuka da dama sannan da dama kuma sun samu raunuka sakamakon mamakon ruwan sama da aka zabga a Afghanistan.

“Abin bakin ciki, ɗaruruwan ‘yan kasarmu ne suka mutu a wannan mummunar ambaliyar ruwa, yayin da adadi mai yawa suka samu raunuka,” in ji kakakin gwamnatin Zabiullah Mujahid a ranar Asabar, ba tare da bayyana adadinsu ba.

A daidai lokacin da ake fama da bala’in ambaliyar ruwa a larduna da dama waɗanda suka haɗa da Badakhshan da Baghlan da Ghor da Herat, gwamnatin Afghanistan ta nuna alhininta ga iyalan da suka samu kansu cikin wannan bala’i tare da alƙawarin bayar da taimako agare su, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan yawon buɗe ido da dama ne suka maƙale sakamakon ambaliya a Kenya

“Ambaliyar ta yi ɓarna sosai a kan ƙadarori da gidaje da dama, wanda ya haifar da asarar kuɗaɗe masu yawa,” in ji shi.

Mujahid ya buƙaci mazauna ƙasar da su taimaka wurin kai kayan agaji ga waɗanda suke buƙata a irin wannan lokoaci.

Ambaliyar ruwa ta samu sassa daban-daban na Afghanistan inda hukumomi a Juma’ar da ta gabata suka ce aƙalla mutum 50 sun rasu.

Leave a Reply